Jam’iyyar adawa ta PDP, ta bayyana cewar tsananin yunwa da ’yan Najeriya ke ciki ne ya haifar da zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a watan da ya gabata.
Daga ranar 1 zuwa 10 ga Agustan 2024, ’yan Najeriya da ƙungiyoyi daban-daban sun fantsama kan tituna domin zanga-zangar nuna rashin jin daɗin yadda matsalolin rayuwa da suka addabi al’umma.
- ’Yan bindiga sun sace ma’aikatan jinya da marasa lafiya a Kaduna
- Ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta
A lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar a Abuja a ranar Litinin, Sakataren Yaɗa Labaran PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa yunwa ce ainihin musabbabin zanga-zangar, ba wasu mutane ba.
Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta mayar da hankali wajen magance yunwa maimakon kama wasu da sunan waɗanda suka ɗauki nauyin zanga-zangar.
Ologunagba, ya bayyana haka ne, bayan kama Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajearo da DSS ta yi a ranar Litinin.
Ya ce, “Gwamnati tana buƙatar sake dabaru. Mutane sun yi zanga-zanga, maimakon a magance matsalolinsu, sai aka ɓige da kama wasu ana cewa ’yan ta’adda ne, kuma aka ce wasu ne suka ɗauki nauyin zanga-zangar.
“Mun san abin da ya haifar da zanga-zangar—yunwa ce. Gwamnati ta mayar da hankali wajen magance wannan, sai matsalolin su ƙare.
“Manufofin gwamnati masu tsauri suna ƙara jefa mutane cikin wahala. Yanzu za a fara komawa makarantu kuma duk muna ganin irin halin da mutane ke ciki.”