✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

YouTube zai biya wadanda aka kalli bidiyonsu kudi

Shafin YouTube zai biya wasu mamallakan hotunan bidiyo da mutane suka biya kudi kafin su kalla, a lokacin da shafin ya yi gwajin tsarinsa na…

Shafin YouTube zai biya wasu mamallakan hotunan bidiyo da mutane suka biya kudi kafin su kalla, a lokacin da shafin ya yi gwajin tsarinsa na karbar kudin kallo a wurin jama’a, kamar yadda BBC ya bayyana.

A ranar Laraban makon jiya shafin na YouTube ya kaddamar da tsarin biyan kudi a wata a Amurka kafin mutane su kalli wasu hotunan bidiyo da shafin ya cire tallace-tallace a cikinsu.
Shahararrun masu sanya hotunan bidiyo a shafin sun nuna damuwa kan cewa shafin ba zai biya su ba idan ya karbi kudi daga wurin jama’a na kallon bidiyonsu a wata daya da zai yi yana gwaji.
Masu sanya hotunan bidiyo a shafin suna samun kudi daga tallace-tallacen da ake nunawa a cikin bidiyon, amma sabon tsarin da shafin ya bullo da shi, ya cire tallace-tallace a Amurka saboda biyan kudi da jama’a suka yi.
A maimakon samun kudin daga tallace-tallacen, shafin na YouTube zai dan nuna musu hotunan bidiyon da aka kalla kadan daga cikin kudin da ya samu, gwargwadon mintocin da aka kalle su