✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

YouTube da Gmail sun samu matsala

YouTube da Gmail sun samu matsala a kasashen duniy a dama

Miliyoyin masu amfani da manhajojin kamfanin Google da suka hada da Gmail, Google documents, YouTube da sauransu a kasashe da dama sun samu tsaikon amfani da su, yayin da mahajojin suka samu matsala a ranar Litinin.

Sai dai masu gudanar manhajar YouTube sun bayyana a shafinsu na twitter cewa “Muna sane da irin matsalar da masu mu’amala da mu ke fuskanta wajen amfani da YouTube, muna kokarin ganin komai ya daidaita”.

Mutane da dama daga kasashe daban-daban sun shiga kafafen sada zumunta musamman Twitter da Facebook inda suka dinga bayyana rashin jin dadinsu na kasa amfani da manhajojin.

Sai dai duk da wannan matsala da aka samu game manhajojin kamfanin Google, wasu daga cikin manhajojin kamar Google Chrome, Google Maps da kuma sashen neman bayanai na Google duk sun yi aiki ba tare da tangarda ba.