Kamfanin Meta, mamallakin Facebook, ya amince zai biya dala miliyan 25 don sasantawa kan shari’ar da Donald Trump, ya shigar game da rufe shafinsa.
Trump, ya maka Meta a kotu a shekarar 2021 bayan da Facebook ya rufe shafinsa sakamakon harin da aka kai Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairu.
- Masu ɗibar fetur daga tankar da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara hari
- DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen M23 —Shugaba Tshisekedi
Kaso mafi tsoka na kuɗin wanda ya kai dala miliyan 22—zai tafi ne wajen gina ɗakin karatu na Trump, yayin da sauran ƙudin za a biya lauya da wasu mutane da suka shigar da ƙarar tare da shi.
Trump, ya kuma maka Twitter (wanda yanzu ake kira X) da YouTube a kotu saboda rufe shafukansa, amma kotu t kori ƙarar.
A baya, Facebook ya dakatar da Trump saboda yaɗa labaran ƙarya kan zaɓen Amurka na 2020, amma daga baya ta rage takunkumin zuwa shekaru biyu, sannan ta dawo masa da shafukansa a shekarar 2023.
Rahotanni sun ce tattaunawar sulhu ta fara ne a watan Nuwamban 2024 lokacin da Shugaban Kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, ya gana da Trump a gidansa na Mar-a-Lago.
Bayan wats tattaunawa da suka yi a watan Janairun 2025, Meta ta amince da cire wasu takunkumai da aka ƙaƙaba wa shafukan Trump.
Trump, wanda shi ne sabon shugaban Amurka, a baya ya yi amfani da shafukansa na sada zumunta wajen jadadda iƙirarin cewar shi ne ya lashe zaɓe 2020 da aka gudanar a ƙasar.