Kamfanin Meta, wanda ke kula da Facebook, Instagram, da WhatsApp, ya bayyana cewa wata matsala ta haifar da tasgaro wajen amfani da kafafen sadarwar.
A Amurka, sama da mutum 100,000 ne suka bayyana cewar suna fuskantar matsala a Facebook.
- Abba ya bai wa Hajiya Mariya Galadanchi tallafin N2m
- Mutum 6 sun mutu a wani sabon hatsarin mota a Jigawa
Haka kuma, dubban mutane a faɗin duniya na fama da matsaloli wajen amfani da kafafen da kamfanin na Meta ke kula da su.
Meta ya wallafa wani saƙo a shafinsa na X, inda ta ce: “Muna sane da cewa wata matsala ta fasaha tana shafar mutane wajen amfani da manhajojinmu.
“Muna aiki tuƙuru don magance matsalar cikin ƙanƙanin lokaci, kuma muna bayar da haƙuri kan wannan rashin jin daɗin.”
An fara fuskantar matsalolin ne da misalin ƙarfe 6 na yamma.
A Birtaniya, sama da mutum 25,800 ne suka kasa amfani da Facebook, yayin da mutum 15,500 suka fuskanci matsala s WhatsApp.
A Amurka, sama da mutum 106,400 ne suks bayar da rahoton samun matsala da Facebook.
A Najeriya ma, dubban mutane ne duka shiga bayyana damuwarsu kan yadda manhajojin suka samu matsala.
WhatsApp ya kuma wallafa saƙo a shafin X cewa: “Muna aiki don magance matsalar kuma mun fara ganin al’amura sun fara daidaita.
“Muna sa ran komai zai dawo yadda ya kamata nan ba da jimawa ba.”
Har ila yau, Instagram ya bayyana cewa: “Mun san cewa wasu masu amfani da manhajarmu suna fuskantar matsaloli wajen shiga Instagram.
“Muna aiki don gyara matsalar, kuma muna bayar da haƙuri kan wannan lamari.”
Wannan ba shi ne karo na farko da manhajojin Meta ke samun matsala ba.
A farkon wannan shekarar, wata matsala ta haifar wa masu amfani da Facebook da Instagram tsaiko.
A watan Oktoba ma, irin wannan matsalar ta faru, amma an gyara ta cikin awa ɗaya.