✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi

Ya amsa cewa a Facebook ya haɗu da ita, daga bisani ta ziyarci ɗakinsa, inda ta gamu da ƙarar kwana

Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan.

Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa.

Ya shaida musu cewa a Facebook ya haɗu da ita, inda daga bisani ta ziyarci ɗakinsa a unguwar Olunlade a garin Ilori, bayan ta je wani biki.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa na kashe ɗalibar mai suna Hafsah Yetunde Bello domin yin tsafi.

A cikin bidiyon tambayoyin da ’yan sanda ke wa matashin mai suna Abdulraham Bello, ya ce bayan zuwan budurwar tasa ne ya je ya sayo mata abinci, bayan ta bayyana masa cewa tana jin yunwa.

Ya shaida wa masu binciken nasa cewa bayan ya dawo daga sayo abincin ne ya iske ta tana shassheka a ɗakin.

“Ba a jima ba sai ta mutu. Ni kuma na tsotsa, babu wanda zan iya zuwa gaya wa ya taimaka min, shi ne ne sassara gawarta na yi mata gunduwa-gunduwa na je na jefar a wata bola a unguwar.

“A rikice nake, ban san abin da zan yi ba, ko tunanin wata hanya ta daban. Amma ban taɓa yin haka ba, wannan ne karon farko,” in ji matashin a ofishin ’yan sanda.

A cikin bidiyon da ya yi jawabin nasa cikin harshen Yarbanci ya bayyana cewa a halin yanzu yana neman gurbin karatu ne a Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Malete.

Mamaciyar dai ɗalibar aikin ƙarshe ce a Kwalejin Koyarwa ta Jihar Kwara.