Musa Mustapha, surukin tsohon Gwamna Yobe kuma Ministan Harkokin ’Yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam, ya lashe zaben dan takarar Jami’yyar APC na zaɓen cike gurbin Sanata Yobe ta Gabas.
Mustapha Musa wanda shi ne mahaifin matar Sanata Ibrahim Gaidam ya lashe zaben fidda gwanin ne da nufin maye gurbin mijin ’yarsa, wanda Shugaba Tinubu ya naɗa Ministan Harkokin ’Yan Sanda, a kujerar Sanata.
Aminiya ta ruwaito cewa surukin na Gaidam ya yi nasara ne da kuri’u 356 inda ya doke abokin karawarsa, Dokta Salisu Sanda wanda bai samu ko da kuri’a guda ba, a zaɓen da aka gudanar a garin Damaturu ranar Asabar.
A jawabinsa na lashe zabe, Musa Mustapha ya “gode wa Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon bayan da yake ba wa jam’iyyar da kuma wakilan jam’iyyar kan abin da suka yi don ganin an gudanar zaben cikin nasara.”
- An kashe mutanenmu 350 a Filato —Kungiyoyin Fulani
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Kauce Wa Talauci A Watan Janairu
Za a gudanar da zaben cike gurbi ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2024 in Allah Ya kai mu.
Kafin yanzu, Alhaji Musa Mustapha dai shi ne Kwamishinan Sufuri da Makamashi na Jihar Yobe kuma tsohon kwamishinan kudi a zamanin mulkin Sanata Gaidam.
Tun kafin zaben dan takarar labari ya karade jihar kan cewar, Mustapha Musa shi ne wanda tsohon gwamnan ya nuna a matsayin wanda zai gaje shi a kujerar Sanata.
Yanzu abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a zaben cike gurbin, musamman atsakanin Jam’iyyar APC mai mulkin jihar da kuma babbar jami’yyar adawa ta PDP.