✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

 Yin ’yar tafiya bayan cin abinci yana maganin Ciwon Suga – Masana

Yin tattaki na minti 2 yana taimakawa

Wasu kwarrarrun masu bincike kan lafiya sun gano cewa yin ‘yar tafiya ko tsayuwa bayan cin abinci na da matukar fa’ida ga lafiyar masu fama da Ciwon Suga.

Binciken masanan ya gano cewa yin tattaki na kimanin mintuna biyu bayan cin abinci na saukar da yawan sukarin da ke jinin mutum, ya kuma rage masa hatsarin kamuwa da Ciwon Suga mai nau’in ‘type 2.

Wasu masu bincike a Jami’ar Limerick da ke Ireland ne suka gano hakan bayan nazarin sakamakon wasu gwaje-gwaje da aka yi guda bakwai.

Gwaje-gwajen na wadanda suka zauna ne, da wadanda suka yi ‘yar tafiya, da kuma wadanda suka tsaya a tsaye bayan cin abinci.

Gwajin da aka yi musu na duba lafiyar zuciya da sinadarin Insulin a jiki da kuma yawa sukarin da ke cikin jininsu ne.

An kuma gano cewa yin ‘yar tafiya bayan cin abinci da suka yi, ya yi matukar tasiri wajen daidaita yawan sukarin da ke cikin jinin jikinsu.

Dakta Aiden Buffy jagorar binciken da aka wallafa a mujallar likitanci na wasannin motsa ciki ya ce,  “dan tatattaki na minti daya ko biyu ya fi zama fa’ida da tashi ka dafa cofee ne ka dawo ka zauna, ko kuma zuwa kofar ofishinka ka dawo.

Wani likitan kula da lafiyar Zuciya Dakta Euan Ashley na Jami’ar Stanford na cewa, “ko da ba za ka iya zuwa ko ina ba saboda yanayin aiki, ka tashi tsaye [bayan cin abinci] zai taimakawa lafiyarka matuka.