✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yi wa fasinja fyade: Kotu ta yi wa dan acaba daurin rai-da-rai

Ta dauki hayar babur dinsa zuwa gida, shi kuma a hanya ya yi mata aika-aikar.

Kotu ta yanke wa wani dan acaba da ya yi wa fasinjarsa fyade a kan hanya hukuncin daurin rai-da-rai.

Dan acabar ya yi wa wata matashiya fyade da karfin tsiya ne bayan dawowarta daga coci, inda ta dauki hayar babur dinsa zuwa gida, shi kuma a hanya ya yi mata aika-aika.

Kotun ta ce ta yanke mishi hukuncin ba tare da zabin biyan tara ba ne bayan ta same da laifin keta mutuncin fasinjar tasa mai mai shekara 21.

Da yake sanar da hukuncin zaman wakafi na rai-da-rai, alkalin Babbar Kotun Jihar Legas da ke zamanta a Oshodi ta ce, ya ce masu gabatar da kara sun bayar da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da laifin wanda ake zargi.

Bayan haka ne lauyan da ke wakiltar wanda ake kara, Barista Ramon Bashir, ya bukaci kotun da ta sassauta mishi, domin a baya bai taba aikata wani babban laifi ba.