✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yesu: Mai ceton duniya (2)

Dalilin zuwan Yesu duniya Ina so mu fara a yau da yin wannan tambaya. Wane ne ya halici duniya da abin da ke cikinta? Za…

Dalilin zuwan Yesu duniya

Ina so mu fara a yau da yin wannan tambaya. Wane ne ya halici duniya da abin da ke cikinta? Za mu samu amsa a cikin Littafi Mai tsarki. A rubuce yake a Farawa sura 1, aya 1 cewa: “A cikin farko Allah Ya halitta sama da kasa.” Littafin Farawa sura 1 ya ba da jerin halittu na dukan duniya da abubuwan da ke cikinta, wanda Allah Ya yi a cikin kwanaki shida. Aya ta 31 wadda ita ce aya ta karshe na wannan sura ta ce, “Allah kuwa Ya ga dukan abin da Ya yi, ga shi kuwa yana da kyau kwarai. Ga maraice, ga sfiya, kwana na shida ke nan.” Allah Ya yi wannan duniya da kyau da kuma kawa –sai Ya damka ta a hanun mutum domin ya mallake ta. A cikin sura ta biyu ta Farawa din, an rubuta cewa Allah Ya ba da umarni ga Adamu game da itaciyar da ke cikin tsakiyar gona, cewa kada ya ci daga ’ya’yanta domin kada ya mutu. Sai mutum ya yi zaɓi mara dacewa, ya kama gaban kansa ya ci ’ya’yan wannan itacen. Alamun farko na la’anar da ta fado kan mutum bayan da ya yi tawaye ga umarnin Allah, su ne, tsiraici, tsoro, (fargaba da razana) da kunya. Farawa sura 3, aya 7–9 na cewa: “Sai dukansu biyu idanunsu suka bude, sa’an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka dindinka suka yi wa kansu sutura. Da suka ji motsin Allah Yana yawo a gonar da sanyin la’asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. Amma Ubangiji Allah Ya kira mutumin, Ya ce, ‘Ina kake?’ Sai ya ce, ‘Na ji motsinKa cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”  
Biye da wannan sai muka ga shigowar kiyayya a duniya. Wannan yana bayyane a aya ta 15 inda Allah Ya fuskanci makiyin, wato Iblis da zancen zuwan wanda zai hallakar da shi: “Zan sa kiyayya a tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai kuje kanka, kai za ka kuje duddugensa.”
Hatta, ciwon nakuda ga mata bayyanuwar la’ana ce da zunubi ya jawo a kan dan Adam. A aya ta 16 mun ji Allah Yana furci ga ita matar Adamu, wato Hauwa’u da cewa: “…zan tsananta nakudarki ainun, da azaba za ki haifi ’ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”  
La’anar da ta shigo duniya ba ta tsaya a kan mutum kadai ba; ta shafi dukan halittu a doron kasa. Alamar la’ana ta farko da ta fado a kan kasa ita ce tsirowar kayoyi da sarkakiya. Littafi ya ce “Ga Adamu kuwa Allah Ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ’ya’yan itacen da na doka ce ka, kada ka ci daga cikinsa.” Tunda ka aikata wannan za a la’antar da kasa saboda kai da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka. kayoyi da sarkakiya za taba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar.”
A sanadin la’anar da ta sauko a kan kasa sai albarkar da Allah Ya shimfida domin ta ba da abinci ga mutum ta dage, sai ya zamana ta wurin ci da gumi mutum zai iya ya ciyar da kansa. Littafi ta ce, “Za ka yi zufa da aiki tukuru kafin ka samu abinci…” Farawa 3 :19a ; sa’an nan daga karshe kuma mutum zai koma ga kasa, aya 19 ta ce, “…har ka koma ga kasa, gama da ita aka siffanta ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.”
Babban masifar da ta samu mutum ita ce korarsa da aka yi daga fuskar Allah. A rubuce take a cikin nassi cewa, “Domin haka Ubangiji Ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan… Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko’ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.” Farawa 3:23-24.
Bayan wannan kora, sai Adamu da Hauwa’u suka yi rayuwa bisa azancin kansu a cikin kunci da wahalhalu daban-daban, zunubi kuma sai ya ci gaba da yaduwa har ya mamaye zukatan dukan mutane. Ba da jimawa ba sai Kayinu, dan fari na Adamu ya zama mai kisan kai har ya kashe kanensa Habila. Bayan wannan kuma sai zunubi ya yadu ya cika zukatan dukan mutane har sai da Allah Ya shar’anta duniya ta wurin ambaliyar ruwa da hallaka dukan abu mai numfashi a doron kasa. Wadanda suka tsira, mutum takwas ne kacal, wato Nuhu da matarsa da ’ya’yansa uku da matansu, sai kuma dabbobin da Allah Ya umurci Nuhu ya shigar da su a cikin babban jirgin ruwa da Allah Ya umurce shi ya gina.
Yanzu a fili yake cewa komai ya riga ya kama hanyar gurɓacewa. Wannan kwayar zunubi daya da Adamu ya aikata ita ta zama sanadin hayayyafar mugunta da lalacewa a duniya. Duk muguntar da ke akwai a duniyar nan tana da tushe a cikin zuciyar mutum –kisan-kai, husuma, yaki, raini, zina, fasikanci, gulma, keta, zargi, da sauransu suna da tushe ne a cikin zuciyar mutum. Yesu ya ce a littafin Matiyu 15:18-19, “Amma abin da ya fito ta baki, daga zuci yake, shi ne kuwa yake kazantar da mutum. Don daga zuci mugun tunani ke fitowa, kamar su kisan-kai da zina da fasikanci da sata da shaidar zur da yanke. ”
Mun gani, dukan ayyukan mugunta suna da tushensu a zuciyar mutum, saboda haka idan har mutum zai sauya rayuwarsa ba zai kasance ta wurin aikin ibada ba; dole ne sai ya samu sabuwar zuciya da farko wadda za ta fito da sababbin halaye, akasin zuciyar mai mugunta wanda aka haifi kowa da ita.
Tambaya ita ce, mutum zai iya ya sauya wa kansa zuciya? Amsa a fili take –a’a. Shin akwai likita wanda ya kware a aikin tiyati da zai iya ya yi wa kansa fida? Wannan shi ne dalilin da ya sa Allah Ya aiko da Yesu Almasihu domin ya yi wa dukan’yan Adam tiyatar zuciya.
Duniya tana bukatar ceto domin ta rigaya ta kama hanyar shiga halaka. Koda bayan hukuncin da duniya ta samu a zamanin Nuhu, mutane sun ci gaba da kangarewa. Mugunta ta ci gaba da haɓaka, har ma Littafi ta bayyana mana a fili cewa, “Gama ’yan Adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga daukakar Allah.” Romawa 3:23.
Mutum ba ya da iko ya ceci kansa. Babu aikin ibada wanda zai yi da za ta fisshe shi daga ikon halaka. Saboda haka Allah a cikin kaunarSa mara bambanci Ya shirya hanyar ceto ga dukan mutane. Idan har duniya za ta tsira, lallai sai idan Allah da kanSa Ya shirya hanyar tsirar. Wannan hanya Ya shirya ta a cikin Yesu Almasihu. A cikin nazarinmu na farko a kan ASALIN YESU ALMASIHU, Mala’ika Jubrilla ya kawo sakon haihuwar Yesu mai ceto ga uwarsa Maryama. “Mala’ikan kuma ya ce mata, “kada ki ji tsoro, Maryamu, kin samu tagomashi a wurin Allah. Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi da, ki kuma sa masa suna Yesu.” Luka 1:30-31.
 Bayan da aka haifi Yesu sai wani mala’ika ya kawo sakon haihuwarsa ga wadansu makiyaya a saura. Nassi ya ce, “Sai mala’ikan ya ce musu, “kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. Domin yau an haifa muku mai ceto a birnin Dauda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.” Luka 2:10-11.