✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu

Mun hari manyan masana nukiliyarsu, sannan har yanzu muna da sauran aikin da za mu yi a daya bangaren.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo ƙarshen rikicin ne.

A wata hira ta tsawon minti 20 da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi, Netanyahu ya kare matakin farmakin da ƙasarsa ta kai wa Iran, inda ya kwatanta jagoran addini Khamenei a matsayin wani sabon Hitler na wannan zamani.

A yayin hirar, duk wata tambaya da aka yi masa game da ko Shugaban Amurka Donald Trump ya sahale wa Isra’ila kan shirin kashe babban jagoran addinin, Netanyahu ya ki kawar da yuwuwar hakan.

Da aka matsa shi a kan ko za su hari jagoran, sai ya ce : “Muna yin abin da muke da bukatar yi.”

“Mun hari manyan masana nukiliyarsu, sannan har yanzu muna da sauran aikin da za mu yi a daya bangaren.”

Netanyahu ya nuna cewa sun kai wa Iran hari ne domin kare al’umma, domin kare duk wata barazanar nukiliya daga Iran.

Firaministan a hirarrakin da ya yi da kafofin yada labaran Amurka a kwanakin nan, ya bayyana rikicin Isra’ila da Iran a matsayin “yakin wayewa da dabbanci.”

Ya ce akwai bukatar Amurkawa su damu matuka game da kokarin da Tehran ke yi na mallakar makamin nukiliya da karfinta na makami mai linzami.

“Idan yau birnin Tel Aviv ne, gobe kuma New York ne,” kamar yadda Netanyahu ya shaida wa wakilin ABC, Jon Karl.

AFP