Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta.
Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada.
- Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman
- ‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’
Netanyahu ya ce ya yi ganawa ta awa huɗu da majalisar yaƙinsa inda kowa ya bayyana kaɗuwa da halin da mutane uku da Hamas ta saka ranar Asabar suka kasance.
“Dukkanin mu mun yi maraba da buƙatar shugaba Trump na sakin mutanen zuwa ranar Asabar da rana, sannan za mu yi maraba da shirin da shugaban yake da shi na makomar Gaza.
“Bisa la’akari da sanarwar da Hamas ta fitar na karya yarjejeniyar tare da ƙin sakin waɗanda ake garkuwa da su a jiya da daddare, na umarci IDF da su haɗa kan sojoji a ciki da kewayen Gaza.
“Shawarar da muka yanke a majalisar ministoci ita ce idan har Hamas ba ta dawo mana da waɗanda take garkuwa da su ba zuwa ranar Asabar, za a kawo ƙarshen yarjejeniyar kuma dakarun IDF za su koma yaƙar Hamas har zuwa lokacin da za a samu galaba a kansu,” in ji Netanyahu.
Mun dakatar da sakin fursunonin Isra’ila — Hamas
A jiya Litinin ce Hamas ta sanar da yanke shawarar jinkirta sakin fursunonin Isra’ila nan gaba har sai abin da hali ya yi.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta fitar tana mai cewa an ɗauki matakin ne a matsayin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi.
Sanarwar da ɓangaren sojin Hamas ɗin ya fitar ta ce “fiye da mako uku, shugabacin ƙungiyar na bibiyar yadda maƙiya suka gaza cika ka’idojin yarjejeniyar da suka cimma.
“Karya wannan ƙa’ida, har da jinkirta dawowar waɗanda suka rasa muhallansu zuwa Arewacin Gaza, inda ake fakon su tare da harbin su, da harba musu bama-bamai, a yankuna daban-daban na Gaza, wanda hakan ke nuni da yadda suka gaza ƙyale ayyukan jinƙai, da sauran yarjejeniyar da suka cimma tunda farko.
“Baya ga nan, dakarun na Hamas tun farko sun mutunta wannan alƙawari da aka yi.
Saboda haka Hamas ta ce “sakin ƙarin wasu masu rajin kafa ƙasar Yahudawa a ranar Asabar, 25 ga watan 2025, sun dakatar da shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran maƙiya, za su fara mutunta yarjejeniyar da aka cimma da aka fara aiwatarwa makonin da suka gabata.
“Muna sake jadada aniyarmu ta ci gaba da mutunta dukkan yarjejeniya da ka’idojin da aka gindaya, idan har masu mamayar suka bi su sau da ƙafa.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 24 a yau Talata.
Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 48,180, inda a yanzu aka sauya alƙaluman zuwa 62,000 saboda an ayyana waɗanda suka ɓata a matsayin matattu.
Trump ya yi barazanar soke yarjejeniyar
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai soke yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sannan ya bari “ko ma mai zai faru ya faru” idan ba a saki Isra’ilawa da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su ba daga yanzu zuwa ranar Asabar.
“A ganina, idan ba a saki mutanen da aka yi garkuwa da su ba daga yanzu zuwa ranar Asabar da ƙarfe 12 na rana, zan soke yarjejeniyar sannan na bari duk abin da zai faru ya faru,” in ji Trump.
“Muna so a dawo da su. Ina magana ne a ƙashin kaina. Isra’ila tana iya ƙin amincewa da hakan, amma dai ni a ganina, ranar Asabar da ƙarfe 12 na rana, idan ba a sake su ba, za a yi babban bala’i.”
Isra’ila ce ta karya yarjejeniyar — Erdogan
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce Isra’ila ta “gaza cika alƙawurran da ta ɗauka” dangane da yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza.
Erdogan ya ƙara da cewa “dole ne mamayar Isra’ila ta zo ƙarshe. Mamayar da suke ce ƙashin bayan duk wata matsala.”
Erdogan ya kuma ce zai aike da tallafin kayan agaji zuwa Gaza, inda ya yi kira da aka kafa ƙasar Falasɗinawa mai cin gashin kanta.