✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gano gawarwakin Isra’ilawa 6 da aka yi garkuwa da su a Gaza ya tayar da ƙura

Netanyahu bai damu da rayuwar kowa ba, ciki har da fursunonin Isra’ila.

Ba’amurke Hersh Goldberg-Polin, wanda iyayensa a kwanan nan suka yi magana a DNC, na cikin waɗanda aka gano gawarsu a wani rami a yankin Rafah.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta gano gawarwakin mutum 6 da aka yi garkuwa da su, ciki har da na Ba’amurken.

Ɓullar wannan labari ya haifar da zanga-zanga a Isra’ila tare da sake kiran tsagaita wuta.

Mutanen da aka yi garkuwa da su, waɗanda rahotanni suka ce an gano su a wani rami da ke yankin Rafah, a Kudancin Gaza, na daga cikin mutum 250 da Hamas ta yi garkuwa da su a harin da aka kai a Kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ’yan Isra’ila 1,200.

Sama da Falasɗinawa 40,000 ne aka bayar da rahoton Isra’ila ta kashe a yaƙin da take yi a Gaza a matsayin martani ga hare-haren.

Daga cikin waɗanda suka mutu akwai Ba’amurke Hersh Goldberg-Polin, wanda iyayensa suka yi jawabi a babban taron Jam’iyyar Democrat a watan jiya kuma suka jagoranci ƙoƙarin ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

An shirya sakin uku daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, a cewar CNN.

Kimanin mutum 100 da aka yi garkuwa da su ne suka rage a Gaza, kodayake sojojin Isra’ila sun ce an kashe da dama daga cikinsu.

An gano gawar Goldberg-Polin tare da na Eden Yerushalmi, Alexander Lobanov, Almog Sarusi da Ori Danino, waɗanda aka sace su a lokacin bikin kiɗa na Nova a ranar 7 ga Oktoba.

An ɗauki wata ta shida da abin ya shafa, Carmel Gat, daga wata unguwar manoma da ke kusa, a cewar Kamfanin Dillacin Labarai na Associated Press.

Wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa an kashe waɗanda aka yi garkuwa da su ne ta hanyar harbi, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Isra’ila.

An ba da rahoton cewa an kashe su ne ’yan sa’o’i kaɗan kafin a gano su a cikin wani rami, mai tazarar rabin mil daga ramin da aka gano ɗan Isra’ila, Farhan al-Ƙadi da ransa a makon jiya.

Sai Ƙungiyar Hamas ta yi iƙirarin cewa mutum shidan da aka kashe sun mutu ne sakamakon wani harin da aka kai ta sama ta hanyar amfani da makaman da Amurka ke ɗaukar nauyi.

Su wane ne mutum 6 da aka kashe?

  • Hersh Goldberg-Polin, mai shekara 23

Wani ɗan asalin Berkeley, na Jihar Kalifoniya wanda ya rasa wani ɓangare na hannunsa yayin harin na 7 ga Oktoba. Iyayensa Jon Polin da Rachel Goldberg sun kasance fitattun masu fafutikar ganin an sako waɗanda aka yi garkuwa da su, inda suka gana da shugabannin duniya kamar Shugaba Biden da Paparoma Francis.

  • Eden Yerushalmi, 24

Wata mai koyar da kiɗan Pilates da aka haifa a Tel Aviv wacce ke yin kiɗa a bikin Nova lokacin da aka kama ta.

  • Karmel Gat, 40

Wata ma’aikaciyar aikin jinya ce daga Tel Aviv wacce aka sace daga Kibbutz Be’eri, inda aka kashe iyayenta.

  • Alexander Lobanov, 33

Mahaifin yara biyu ne da aka sace daga bikin Nova, inda ya yi aiki a matsayin manajan mashaya. Rahotanni sun ce ya taimaka wa wasu tserewa yayin harin kafin a kama shi.

  • Almog Sarusi, 27

An kama shi ne bayan ya zauna tare da budurwarsa da aka raunata a lokacin harin da aka kai bikin, inda aka kashe ta.

  • Ori Danino, 25

An yi garkuwa da Danino a cikin yara biyar yayin da yake taimakawa wasu suna tserewa daga bikin Nova.

An gudanar da zanga-zanga da yajin aiki a Isra’ila

Magajin garin Tel Aviv, Ron Huldai ya sanar a cikin wata sanarwa da aka watsa a shafukan sada zumunta cewa birnin ya shiga yajin aiki, don nuna goyon baya ga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, inda ya soki gwamnatin Isra’ila, wanda ya yi iƙirarin cewa ta yi watsi da su.

Ƙungiyar Hostages and Missing Families Forum, wata ƙungiya mai fafutika da ke wakiltar ’yan uwa da dama da aka yi garkuwa da su a Gaza, ta soki Firayi Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta NBC ta ruwaito, kuma ta buƙaci duk ’yan Isra’ila da su shiga zanga-zanga don yin matsayin lamba kan Majalisar Ministocin Ƙasar da kuma Firayi Minista don a tsagaita wuta.

A cewar NBC News, za a gudanar da wani shiri don girmama waɗanda suka rasa rayukansu a Gaza.

Aƙalla mutum 700,000 ne suka halarci zanga-zangar a aka yi a duk faɗin Isra’ila, inda ake kira da a tsagaita buɗe wuta a kuma saki waɗanda akai garkuwa da su.

Babbar ƙungiyar ƙwadago ta Isra’ila ta shiga yajin aiki, tana mai shelar cewa yarjejeniyar zaman lafiya ta fi komai muhimmanci.

Jami’ar Hebrew ta Kudus ta ce ta dakatar da duk wasu ayyuka, in ban da jarrabawa, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su shida, Misis Carmel Gat, ta kammala karatun jami’a, inda ta samu digirin digirgir a fannin aikin jinya.

Netanyahu ya ba da haƙuri ga jama’a

Netanyahu ya nemi afuwar Oksana da Grigory Lobanov, iyayen Alexander Lobanov da aka kashe, yana mai bayyana ɓacin ransa, yana cewa sojojin sun kasa ceto ɗansu da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

“Na yi matuƙar nadama tare da neman gafararku, kan yadda muka kasa ceto ’yan uwanmu da ransu,’’ in ji shi, a cewar wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

An kuma ce Netanyahu ya shirya tautaunawa da iyalan dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, kodayake an ce wasu iyalai biyu sun ƙi amsa kiran nasa.

Biden da Harris sun ce Hamas za ta yaba wa aya zaƙi

Shugaba Joe Biden ya bayyana matuƙar baƙin ciki da fushi bayan samun labarin abin da ya faru, inda ya bayyana Goldberg ­Polin a matsayin matashi marar laifi da aka kashe, ba tare da ya aikata laifin komai ba.

Ya yaba wa iyayensa, waɗanda ya zanta da su ta wayar tarho, bisa jajircewa da juriyar da suka nuna tun bayan hare-haren, inda ya bayyana su a matsayin ’yan kishin ƙasa.

Ita ma Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris ta yi Allah-wadai da abin da Ƙungiyar Hamas ta yi, tana mai bayyana ta da ƙungiyar ta’addanci da ke da alhakin zubar da jinin Amurkawa fiye da ƙima.

Firayi Ministan Biritaniya Keir Starmer, ya kirawo mutuwar tasu da abin takaici da rashin hankali ya kuma ce dole ne dukkan ɓangarorin biyu su amince da yarjejeniyar tsagaita wuta nan take domin kawo ƙarshen wannan wahala da ake ciki.

Trump ya mayar da martani

Tsohon Shugaban Donald Trump ya ce, “Muna baƙin cikin mutuwa ta rashin hankali na Isra’ilawa da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani Ba’amurke Hersh Goldberg-Polin, wanda Hamas ta kashe.”

Trump, ɗan takarar Jam’iyyar Republican a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2024, ya ci gaba da ɗora alhakin mutuwar mutane shida da aka yi garkuwa da su a kan Biden da Harris.

Hamas da shugabannin Falasɗinawa sun zargi Biden

Jami’in Hamas, Izzat al-Rishƙ ya zargi gwamnatin Biden da kisan mutanen shida, yana mai cewa Amurka tana goyon bayan yaƙi da kisan ƙare-dangi saboda son kai na Isra’ila.

“Shugaba Biden, idan yana da sha’awar ceto rayukansu, dole ne ya daina tallafa wa waɗannan maƙiya da kuɗi da makamai tare da matsa musu lamba a kan su kawo ƙarshen ayyukan ta’addancin da suke yi nan da nan,” in ji shi.

Shi ma ɗan Majalisar Falasɗinawa Mustafa Barghouti ya zargi Netanyahu da gwamnatinsa da ƙin amincewa da tsagaita wuta da kuma ɗaukar alhaƙin ta’azzarar rikicin.

A cikin wata sanarwa da aka buga a shafin X, Barghouti ya soki Firayi Ministan Isra’ila da ƙin amincewa a tsagaita wuta.

Ya bayyana cewa Netanyahu ba ruwansa da rayuwar Isra’ilawa da Falasɗinawa.

Ya ce, “Netanyahu bai damu da rayuwar kowa ba, ciki har da fursunonin Isra’ila, kuma damuwarsa kawai ita ce kansa.

(AP)