✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yesu: Mai ceton duniya (1)

Babbar kan maganarmu ita ce, YESU MAI CETON DUNIYA. Duk wanda yake bukatar ceto, nuni ne cewa yana cikin hadari ko yana kan hanyar hallaka.…

Babbar kan maganarmu ita ce, YESU MAI CETON DUNIYA. Duk wanda yake bukatar ceto, nuni ne cewa yana cikin hadari ko yana kan hanyar hallaka. Idan muka dubi duniyar nan da muke ciki za mu gane cewa tana kan hanyar hallaka. Kowane irin mugunta na da tushe a cikin zuciyar mutum : zina, fasikanci, sata, fashi, kwace, zamba, almubazaranci, toshiya, husuma, kiyayya, zalunci kisan kai da sauransu. Muguntar da ke zuciyar mutum ne kuma ta ba da kafa ga bala’o’i daban-daban da suka addabi wannan duniya, wadanda su ka hada da: yaki, cutattuka, girgizar kasa, zaizayar kasa, gusowar hamada, ambaliyar ruwa, mahaukaciyar guguwa da igiyar ruwa, fari da yunwa da dai ire-irensu. Abubuwan da suke faruwa a wannan zamani suna nuni da cewa duniya ta kusa shudewa. Abin da zai hana ta shudewa shi ne idan ta samu wanda zai cece ta. Mai ceton nan shi ne Yesu Almasihu. Akwai abubuwa hudu da za mu yi nazari a kansu game da Yesu Almasihu a cikin wannan bincike. Abubuwa hudun nan su ne:
Asalin Yesu Almasihu
Dalilin zuwansa duniya
Yesu shi ne Hasken duniya
Yesu shi ne Rai

Asalin Yesu Almasihu
Wane ne Yesu Almasihu? Daga ina ne ya fito? Za mu samo amsoshin wadannan tambayoyi daga cikin Littafi Mai tsarki. Bayan da Allah Ya halicci duniya Ya mallakar da ita ga mutum; Ya kuma bar mutum da kashedi game da wata itaciya mai bada ’ya’ya da Ya dokace shi kada ya ci daga ’ya’yanta domin za ta jawo mutuwa. Mutum bai yi la’akari da wannan kashedi ba, ya kama gaban kansa ya ci. Cin itaciyar nan da ya yi shi ne ya zama sanadin zunubin da ya shafi dukan ’yan Adam. Sakamakon zunubi kuwa hallaka ce ta har abada. Bayan shigowar zunubi cikin duniya Allah Ya yi furuci game da wanda zai zo duniya domin ya kawar da Iblis wanda shi ne ya jarabci mutum har mutumin ya rinjaya ya aikata zunubi ga Allah. A cikin Farawa sura 3, aya 15 Allah Ya ce wa magabci (wato Iblis) ‘’Zan sa kiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai kuje kanka, kai za ka kuje diddigensa.’’
Wannan shi ne anabci na farko game da zuwan Yesu Almasihu cikin duniya. A kwana a tashi sai Allah Ya yi kira ga Ibrahim ya bar kasarsa ta asali domin ta wurinsa Yake so Ya cika burinsa na aiko da Mai ceto ga duniya. Ga alkawarin da Allah Ya yi wa Ibrahim a cikin Farawa sura 12, aya 3 dukan iyalan duniya za su sami albarka ta wurinka.
Annabi Ishaya ya yi anabce-anabcen zuwan Yesu Almasihu a cikin wadannan ayoyi:
Ishaya sura 7, aya 14, “Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi da, za a rada masa suna Immanuwel.”
Ishaya sura 9, aya 6:
“Ga shi an Haifa mana da!
Mun sami yaro!
Shi zai zama mai mulkinmu.
Za a kira shi, ‘Mashawarci Mai Al’ajabi,’
‘Allah Madaukaki,’
‘Uba Madauwami,’
‘Sarkin Salama’.”
Ishaya sura11, aya 1-5:
“Gidan sarautar Dauda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sarki daga zuriyar Dauda.
Ikon Ubangiji zai ba shi hikima,
Da sani, da gwaninta yadda zai mallaki mutanensa.
Zai kuwa san nufin Ubangiji,
Ya kuma yi tsoronsa.
Zai ji dadin yin hidimarsa.
Ba zai yi shari’ar ganin ido ko ta waiwai ba.
Zai yi wa matalauta shari’a daidai.
Zai kuma kare hakkin masu tawali’u.
Bisa ga umarninsa za a hukumta kasar,
Mugaye za su mutu.
Zai yi mulkin mutanensa da adalci da mutunci.’’
Annabi Mika ya yi anabci game da garin da za a haife shi. Littafin Mika sura 5, aya 2 ta ce:
“Baitalami cikin Efrata,
Wadda kike ’yar karama a cikin kabilar Yahuza, amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra’ila. Wanda asalinsa tun fil azal ne’’.
A nan muna zancen asalin Yesu Almasihu ne. Ayoyin nan da muka bayar an rubuta su a cikin daruruwa, har ma da dubban shekaru kafin aka haifi Yesu Almasihu. Farawa sura 3 aya 15 ta nuna mana cewa zai zo ne daga mace, sai annabi Ishaya ya yi anabcin cewa budurwa ce za ta haife shi; amma asalinsa, tun fil’azal ne, wato akwai shi tun kafin a haife shi. Tushensa ba a cikin budurwa Maryama ba ne. Kafin aka yi Maryama yana nan. Maryama dai ta zama zababbiya domin shigowarsa duniya.
Muna zancen asalinsa ko! To, a rubuce yake a cikin bishara daga hannun Yahaya 1 aya 1-5:
“Tun fil’azal akwai Kalma, Kalmar nan kuwa tare da Allah take, Kalmar nan kuwa Allah ne. Shi ne tun fil’azal yake tare da Allah. Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuwa abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba. ”
Har ilau, Yesu da kansa ya fayyace wa Yahudawan da ke adawa da shi cewa shi fa, yana nan tun fil’azal. Wannan ma a cikin Littafin Yahaya muka gani, a sura 8, aya 58 inda aka rubuta, “Sai Yesu ya ce masu, ‘lallai hakika ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba ni ne.” Bisa ga zuriyarsa ta mutumtaka, Ibrahim kakan Yesu ne wanda tsakaninsu an yi zamunna arba’in da biyu. Mun gane wannan daga Matta sura 1, aya 1 – 17 inda aka rubuta mana asalin Yesu bisa ga mutumtakarsa. Aya ta ce, “Littafin Asalin Yesu Almasihu, dan Dauda, zuriyar Ibrahim ke nan… ” Wannan aya ta nuna mana cikar alkawarin Allah ga Ibrahim, da kuma cikar anabcin Annabi Ishaya cewa daga zuriyar Dauda zai fito.
Mala’ika Jibrailu ne ya kawo sakon cikar furcin da Allah Ya yi, cewa, daga zuriyar macen mai kuje kan Iblis zai fito, da kuma annabcin annabi Ishaya, cewa budurwa ce za ta haife shi ba tare da tarayya da namiji ba. A cikin Littafin  Matta sura 1, aya 18 – 25 da Luka sura 1, aya 26 – 35 muna da cikakken labarin zuwan Mala’ika Jibrailu da sakon haifuwar Yesu ga ita budurwa Maryama.
Matta sura 2, aya 5 – 6, da Luka 2, aya 1 – 4 sun bayyana mana cikar annabcin Annabi Mika game da garin da aka haifi Yesu.
Burinmu a cikin wannan nazari, shi ne mu fayyace asalin Yesu Almasihu domin mu sami tushen bayyana shi a zaman wanda ya zo duniya ne domin ya kawo ceto ga dukan ’yan Adam. Mun ga asalinsa yanzu. Abu na biye shi ne mu ga dalilin zuwansa duniya.