Wani tsoho dan shekara 70, Cyril Baldock, da ya fito daga garin Bodi da ke Babban Birnin Austiraliya, Sydney, ya sha wani ruwan lemu, inda ya yi ninka da iyo a ruwa, a tsakanin Ingila ta kasar Birtaniya zuwa kasar Faransa, kuma shi ne mutum na farko mai nisan shekaru da ya taba smaun wannan gagarumar nasara.
“Na sha rowan lemu wanda ke dauke da sinadaran magani, don in smau in yi barci,” Baldock ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Austiraliya (AAP), bayan da ya kammala ninkayarsa, sannan tashar talabijin ta Channel wadda ta shirya gasar, ta nuna yadda ya cika ka’idojin gasar.
Baldock ya ce ya yi kokarin cimma wannan buri ne saboda cika mafarkin wanda ya horar da shi, Des Renford, wanda ya yi nufin yin ninkayar, amma sai farmakin ciwon zuciya ya kawo masa cikas. “Des ya so cimma wannan buri, amma al’amarin bai yi wu ba,” a cewar Baldock, kamar yadda ya sanar Cibiyar watsa labarai ta kasar Austiraliya (ABC).
“Na sanar da Des cewa idan na kai shekarun tabbas zan cimma wannan buri,” Sai dai cikin rashin sanina fiye da shekara 30 an kara nisan shekarun da shekara 10, don haka na jira,” inji shi.
Kundin tara bayanai na shahararrun al’amuran duniya, wato Guiness book of Record, akwai yiwuwar ta ya sauya bayanansa, tunda a da wata tsohuwa ’yar shekara 73 daga kasar Austiriliya ta yi yunkurin tsallaka ruwan a cikin makon da ya gabata.
…Yayin da dan shekara 70 ya ci gasar ninkaya daga Ingila zuwa Faransa
Wani tsoho dan shekara 70, Cyril Baldock, da ya fito daga garin Bodi da ke Babban Birnin Austiraliya, Sydney, ya sha wani ruwan lemu, inda…