Sakamakon sanar da ganin jinjirin watan Ramadan din bana da Mai alfarma Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya yi a ranar Lahadi, hakan ya sa aka soma azumin watan Ramadan a ranar Litinin. Musulmin Najeriya sun bi sahun ’yan uwansu na kasashen duniya, wajen azumtar watan na Ramadan, inda suke kaurace wa abinci da abin sha da saduwa da iyali tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana a daukacin watan.
Yin azumin a kowace shekara a watan tara na Kalandar Musulunci, daya ne daga cikin rukunnan addinin Musulunci guda biyar. Kamar yadda Alkur’ani Mai girma ya bayyana. Allah Madaukakin Sarki Ya umarci Musulmi su yi azumi a watann Ramadan, inda Ya ce: “Ya ku waɗanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan waɗanda suke daga gabaninku, tsammaninku, za ku yi taƙawa.” (K2:183).
Bayan kaurace wa ababuwa na zahiri, wajen ci ko sha da sauran iyakokin da aka gitta, a duk tsawon wuni, har ila yau a daya bangaren an hore su da cin ribar watan, wajen nuna dabi’u nagari, kamar: juriya da haba-haba da jama’a da bayar da sadaka tare da kyautatawa, musamman ga jama’ar da ake zaune da su, ba tare da la’akari da addininsu ko kabilarsu ba. Don haka ne ake umurtarsu da bayar da sadakoki da ciyar da marasa galihu tare da gayyatar wadansu, wadanda ko da kuwa ba ma Musulmi ba ne, wajen yin buda-baki tare da su.
A nan muna kira ga Musulmi a wannan muhimmin lokaci su rika la’akari da halin ni-’yasun da wadansu ke ciki, lura da wata ne na rarraba ababuwa tare da nuna ’yan uwantaka.
Dabi’ar yin kyauta da kyautatawa a watan Ramadan, muhimmin abu ne da ke kawo fahimtar juna a tsakanin addinai da zaman lafiyar al’ummomi daban-daban, wanda hakan tamkar wani sinadarin kawo hadin kai ne a zamantakewar kasar nan, musamman a irin wannan lokaci da ake fuskantar irin matsaloli a Najeriya. Azumin kan sa muminin kwarai ya kara zama mai hakuri da juriya. A sa’ilin da Musulmi ya yi azumi, yakan ji zafi ko ba dadi a jiki, amma sai ya cije ya daure da hakan. Kodayake, wannan hanin da kuma dauriyar na wani takaitaccen lokaci ne kawai, amma hakan na sa mutum ya ankara da irin zafin da ke tattare da irin wadannan wahalhalu da mutane da dama ke fama da su, wadanda watakila suna rayuwa cikin bakin talauci, cikin kunci da rashin samun damar muhimman ababuwan da lallai sai da su ake rayuwa.
Hikimar da ke cikin azumtar wannan watan mai alfarma a shekarar Musulunci, ita ce, bukatar Musulmi su zama masu tsantseni da rashin nuna izza a duk al’amuransu na rayuwa. Lallai ne Musulmi su zama masu kiyaye harsunansu daga munanan maganganu da cin naman wadansu da giba da fadar karairayi da gulmace-gulmace da dsauran abubuwan assha. Ana son Musulmi da kada ya zama yana cin abinci mai nauyin da zai iya hana shi yin Kiyamul-Laili, don gudanar da ibada daban-daban kamar nafilfilu da addu’o’i cikin dare.
Ya kamata, Musulmin Najeriya, masu mulki da wanda ake mulkarsu, su yi amfani da wannan dama na watan Ramadan, wajen nisantar duk ababuwan assha da kuma miyagun dabi’u, wadanda suka yi wa kasar daurin huhun-goro na tsawon lokaci, suka kuma hana kasar shiga sahun kasashe masu dogaro da kansu da kuma ci gaba.
Gagarumin halin rashin tsaron da kasar ke fama da shi cikin ’yan shekarun nan, akwai bukatar kowane Musulmi ya nuna halin ya kamata tare da yin abin da ya dace wajen yin hobbasa da kansa don ganin an kawo karshen wadannan matsaloli. Akwai bukatar masu gudanar da wa’azi, su zama masu tsage gaskiya a da’awarsu, kasancewarsu shugabannin al’umma. Kuma lallai ne, su zama masu matukar kula da irin furucin da suke yi, a kan yanayin da kasar ta tsinci kanta a ciki, a halin yanzu. Lallai kuma masu wa’azin su kiyaye kalamai na tunzurawa ko na batanci, a majalisun da suke gudanar da tafsiran Alkur’ani Mai girma. Malaman addinin Musulunci za su ba da gagarumar gudunmawa ta fuskar ilimantar da mabiyansu wajen bin abu hankali, kuma cikin lumana, a kan abubuwan da suke ganin an bata musu ko an shiga hakkokinsu. Ya kamata malaman su kuma yi kira ga kunkiyoyin da suke jan-daga da su rungumi tafarkin zama a teburin sulhu da hukumomi, kamar dai irin babban misalin da Annabi Muhammad (SAW) ya nuna a yarjejeniyar Sulhun Hudaibiyya. Watan Ramadan na bukatar da mutane su barranta daga son rai. Lokaci ne da manyan ’yan kasuwa ke ji lokaci ya yi da za su ci kazamar riba ta hanyar tsuga farashi a kan kayan abinci, wadanda tuni farashinsu ya yi tashin gwauron zabo. Ya kamata su kauce wa wannan mugun tunani wanda hakan zai samar da yanayi mai kyau na wadatar kayayyakin abinci, cikin watan na Ramadan.