Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da kammala dawo da dukkan alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana gida Najeriya daga kasar Saudiyya.
A cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Laraba, ta ce jirgin karshe dauke da alhazai 88 ya bar birnin Jiddah da misalin karfe 10:30 na safe dauke da alhazan jihar Kaduna da Katsina.
- Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos
- Za a fara cin tarar masu shigar banza N50,000 a Delta
A cewar hukumar, hakan ya kawo karshen jigilar da aka shafe kwana 20 ana yi tun ranar 13 ga watan Yuni.
A sakonsa na bankwana ga alhazan, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana godiyarsa ga Allah kan kammala aikin cikin nasara.
Ya kuma bukaci alhazan da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’ar Allah ya kawo mata karshen tarin matsalolin da suke addabar ta.
Farfesa Abdullahi ya kuma tunatar da su cewa Aikin Hajji ibada ce da take nuna zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan ya buƙace su da su ci gaba da zumuncin da suka ƙulla a tsakaninsu lokacin ibadar.