A ranar Lahadin da ta wuce ne kafofin watsa labarai suka bayyana cewa yayar shahararren dan kwallon Italiya Mario Balotelli mai suna Abigail Barwuah ta haifarwa dan asalin Najeriya da yanzu haka yake kwallo a Amurka a kulob din Seattle Sounders jariri.
Seyi Aduloju na hannun damar Obafemi Martins ya tabbatar da labarin haihuwar ga kafofin watsa labarai. Ya ce jaririn namiji ne kuma yana cikin koshin lafiya tare da mahaifiyarsa a lokacin da yake bayar da labarin.
Tun a shekarar bara wato 2012 ce Martins ya tabbatar da soyayyar da ke tsakaninsa da Barwuah a wata hira da ya yi da kafar sadarwar goal.com.
Sai dai wannan shi ne dan Martins na uku amma na farko a wajen Abigail.
A shekarar bara ce masoya biyun suka yi hutun Kirsimati a birnin Legas bayan da aka dauki hotonsu a jirgin da suka yi shata.
Wata majiya ta tabbatar a shekarar bara Abigaiul ta yi barin cikin da take dauke da shi na Martins amma ba ta dade ba ta sake samun wani inda ta haife shi a karshen makon jiya.
Yayar Mario Balotelli ta haifarwa Obafemi Martins da namiji
A ranar Lahadin da ta wuce ne kafofin watsa labarai suka bayyana cewa yayar shahararren dan kwallon Italiya Mario Balotelli mai suna Abigail Barwuah ta…
