✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yana 4 da almajirai 5 sun rasu a gobarar tankar man Jigawa

Ana fargabar yawan mamata bayan hatsarin tankar mai a Jigawa zai ƙaru zuwa 150. Daga cikin mamatan akwai ’ya’ya huɗu na mutum ɗaya da almajirai…

Wani magidanci ya rasa ’ya’yansa hudu a gobarar tankar man da ta kashe mutane sama da 120 a Jihar Jigawa.

Almajirai biyar ’yan makaranta guda da wani dan sanda mai muƙamin Sufeto suna cikin waɗanda qlamarin ya yi ajalinsu.

An binne aƙalla mutane 125 sakamakon fashewar tankar da ɗauke da man fetur a garin Majiya da ke Ƙaramar Hukumar Taura ta Jihar Jigawa.

Gobarar da tashi bayan faduwa da fashewar tankar man ta kuma yi sanda jikkatar aƙalla mutane 75, da a halin yanzu suke samun kulawa a asibiti.

Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta umarci mambobinta su bayar da gudummawa wajen ceto rayuka da kuma jinyar mutanen da abin ya rutsa da su.

Wani mazauna garin, Habu Majiya, ya shaida wa wakilinmu cewa an binne mutane 115 a kabari guda, bayan an sallace su tare da Gwamna Umaru Namadi a kusa da wurin da abin ya faru. Wasu mutun 10 kuma an binne su a wani kabarin.

Shaidu sun bayyana cewa daga cikin mamatan akwai yara almajirai biyar da ’ya’ya huɗu na mutum ɗaya da wani ɗan sanda mai muƙamin Sufeto.

Adadin na iya ƙaruwa

A yayin da jami’an lafiya da ma’aikatan ceto ke ci gaba a aiki, ana fargabar cewa adadin mamatan yana iya kaiwa 150, lura tsananin ƙuna da raunin da waɗanda suke kwance a asibiti.

Al’ummar yankin sun bayyana cewa kusan babu gidan da na za a samu wanda wannan ibtila’i ya shafa ba.

Yadda abin ya faru

A ranar Talata ce wata tanka da ta ɗauki mai daga Kano za ta kai Nguru a Jihar Yobe ta yi ta yi hatsari a a yankin.

Motar ta yi hatsari ne bayan ta kwace daga kan titi a lokacin da direbanta ke ƙoƙarin kauce wa wata mota da ta nufo shi.

Bayan faduwar tankar man ne man da ke cikinta ya tsiyaye, inda mutane suka riƙa tururuwar kwalfar man a cikin mazubai.

Hakan kuwa ya faru ne a daidai lokacin da farashin litar man fetur yake kaiwa N1,400.

Mutanen suna cikin ɗibar man da ke yatsiya ne wuta ta tashi, inda ta babbake aƙalla mutane 125, wasu kimanin 70 kuma suka tsira da munanan ƙuna.

Kakakin ’yan sanda a jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam ya bayan tashin wutar, “Nan take mutane 94 suka mutu, wasu 50 suka kone, inda aka kai su asibitoci daban-daban domin kula da su.

Saba ƙa’idar hanya ne sanadi — FRSC

Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa rashin bin dokokin hanya na daga cikin musabbabin hatsarin.

Kakakin hukumar, Olusegun Ogungbemide, ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a lokacin da direban ya yi ƙoƙarin kauce wa wata kunya a hanyar.

Ya ce sakamakon gudun da motar ke yi ne kan ya fice bayan ya tuntsure, amma direban da yaron motar babu abin da ya same su.

Don haka ya ja hankalin masu ababen hawa da su riƙa kiyaye dokokin hanya.

’Ya’yana hudu sun mutu — Malam Hamza

Wani magidanci mai suna Hamza Ibrahim ya shaida wa wakilinmu cewa ’ya’yansa huɗu sun rasa rayukansu a ibtila’in.

Ya ce ’ya’yan nasa sun haɗa da Yusuf da Sa’idu da Mustapha, wanda ya fara aiki bayan ya samu shaidar difloma a fannin haɗa magunguna.

Malam Hamza ya ce Hassan, wanda mutumin kirki ne, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake ƙoƙarin koro ƙannensa daga wurin da ake kwasar man da ke tsiyaya.

Kanin Malam Hamza mai suna Iliyasu ma ya rasa ɗansa mai suna Yahaya a gobarar, dayan kuma mai suna Abbas yana samun kulawa bayan ƙunar da ya samu.

Almajiraina biyar sun mutu —Alaramma

Alaramma Ibrahim Lawal majiya, malamin wata makarantar tsangaya ne.

Ya bayyana cewa almajiransa biya ne gobarar tankar man ta yi ajalinsu.

Dan sanda ya mutu

Kazalika wani ɗan sanda mai muƙamin Sufeto, Khamisu Habu, na daga cikin mamatan.

Wani mazaunin garin, Abdullahi Salisu, ya rasa kawunsa Tsoho Umar, a lamarin.

’Yan uwansa biyu kuma, Habun Salisu da Murtala Ado, sun samu ƙuna.