✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Ya’yan manyan ’yan siyasa da ke shirin gadar iyayensu

’Ya’yan wadansu gwamnoni da tsofaffin gwamnoni sun bayyana shirinsu na tsayawa takara

A yayin da zaben 2023 yake kara karatowa, ’ya’yan wadansu gwamnoni da tsofaffin gwamnoni sun bayyana shirinsu na tsayawa takarar mukamai daban-daban kamar yadda Aminiya ta gano:

Wadansu daga cikinsu suke son tsayawa takarar kujerun gwamnonin kamar iyayensu, wadansu suna son tsayawa takarar Majalisar Wakilai ne a karkashin jam’iyyun da iyayen suke ciki.

Daga cikin wadannan ’ya’yan manyan ’yan siyasa da suka bayyana niyyarsu zuwa yanzu akwai na Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Ruai da na tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da na tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa da na tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Ahmadu Mu’azu

Kuma a yayin da wadansu suke ganin wadannan ’ya’ya suna da ’yanci kuma suna da dacewar su tsaya takarar wadannan mukamai a matsayinsu na ’yan kasa, wadansu na cewa gwamnonin da tsofaffin gwamnonin suna daukar nauyi tare da ingiza ’ya’yansu su nemi mukaman siyasa ne domin su ci gaba da tatse dukiyar talakawa.

Wadansu manazarta suna da ra’ayin cewa wadansu daga cikin ’ya’yan wadannan ’yan siyasa sababbin yankan rake ne da ba su da wata kwarewa ko masaninya kan mukaman da suke nema, kawai dai suna shiga rigunan iyayensu ne domin su kai ga mukaman siyasarsu.

Dan Sule Lamido na son zama Gwamnan Jigawa

A Jihar Jigawa dan tsohon Gwamnan Jihar kuma jigo a Jam’iyyar PDP Alhaji Sule Lamido yana ta kokarin hayewa kujerar Gwamnan.

Tuni Mustapha Sule Lamido ya sayi fom din neman tsayawa takarar don cim ma burinsa a karkashin Jam’iyyar PDP.

A wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, daya daga cikin masu tallafa masa, Mansur Ahmed, ya ce wani tsohon Minista a Ma’aikatar Harkokin Waje Dokta Nuruddeen Muhammad ya jagoranci wani dandazon magoya baya zuwa Hedikwatar Jam’iyyar PDP ta Kasa don sayen takardar neman tsayawa takarar da ta nuna sha’awa ga Mustapha Lamido.

Dan Bafarawa, Sagir, na son zama Gwamnan Jihar Sakkwato

Kwamishinan Muhalli na Jihar Sakkwato, Alhaji Sagir Bafarawa ma ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar Gwamna a karkashin PDP.

Kwamishinan wanda dan tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa ya bayyana haka ne a wani taro da mambobin Kwamitin Zartawar Jam’iyyar PDP na Jihar.

Ya ce, “Jam’iyya ce kankat a harkar siyasa; wannan ya sa ya gana da shugabannin domin neman tubarrakinsu.

“Kuma shugabannin jam’iyyar sun amince da kudirina na takara kuma ina son tabbatar wa jama’a cewa da yardar Allah in na samu nasara zan dora daga inda Gwamna Tambuwal ya tsaya.

“A matsayina na kwamishina a wannan gwamnati na samu gogewa sosai daga shugabancin Gwamna Tambuwal. Don haka zan ci gaba kan wannan alkibla idan aka zabe ni a matsayin Gwamnan Jihar Sakkwato,” inji shi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Bello Gwaranyo ya yaba wa Sagir Bafarawa kan burinsa na tsayawa takarar Gwamnan.

Ya ce, “Wannan babbar girmamawa ce kuma babban ci-gaba, don haka mun sanya albarka ga burinsa kuma mun amince ya bayyana niyyarsa ta takara.”

Dan Adamu Mu’azu ya shiga takarar Gwamnan Bauchi

Dan tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Ahmadu Adamu Mu’azu, ya bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar a zaben 2023 a karkashin Jam’iyyar PDP.

Ahmed Ahmadu Adamu Mu’azu wanda sunansu daya da na mahaifinsa tuni ya sayi fom din neman tsayawa takara kuma har ya fara kafa harsashin kamfe dinsa.

Darakta Janar na Kwamitin Kamfe dinsa Dokta Kabiru Garba Ilelah, ya ce mai gidan nasa yana son tsayawa takarar ce don ya samar da ayyukan yi da bayar da fiffiko ga kiwon lafiya da ilimi da aikin gona da tsaro da bunkasa karkara da samar da masana’antu a jihar.

Ya ce, matashin ba yana takara da Gwamna Bala Mohammed da keg ado ba ne, wanda yake neman tsayawa takarar Shugaban Kasa.

Ya ce lokaci ya yi da za a samu sauyi a jihar ta yadda matasa za su karbe ragamar shugabanci tare da nuna kwarewarsu wajen iya shugabanci.

Matashin dan Karamar Hukumar Tafawa Balewa da ke Jihar an haife shi ne a ranar 27 ga Fabrairun 1985.

Ya halarci Sakandaren Sojin Sama ta Ibadan, kuma ya halarci Jami’ar Buckingham da ke Ingila inda ya yi digirinsa a Nazarin Kasuwanci, sai kuma ya yi digiri na biyu a Harkokin Kudi a Jami’ar Leicester da ke Ingila.

Pam Jonah Jang zai nemi dan Majalisar Wakilai a Filato

Pam Jonah Jang, dan tsohon Gwamnan Jihar Filato, Jonah Jang, ya shiga jerin ’yan siyasar da suke son tsayawa takarar dan Majalisar Wakilai daga mazabar Jos ta Kudu da Jos ta Gabas a zaben 2023.

Tuni Kwamitin Abokai suka saya masa fom din tsayawa takara a PDP.

A lokacin da suke mika wa Pam Jang fom din a wani biki da aka gudanar a otel din Tamarald Hotel da ke Jos, Dokta Dagwom D Toang ya ce, “Mun zakulo shi ne saboda muna neman ingantaccen wakilci ga al’ummarmu a 2023.

“Mun yi bincikenmu a kan Mista Pam Jang kuma mun gano yana da kyawawan halayen shugabanci da zai wakilce mu a Majalisar Dokoki ta Kasa.

“Wannan ne ya sa muka saya masa fom ta yadda ba zai samu wata dama ta kin bukatarmu ba.”

Dan El-Rufai, Bello na neman dan Majalisar Wakilai

Bello, dan Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga sahun masu neman zama dan Majalisar Wakilai a zaben 2023.

Fostcocin kamfe din Bello a karkashin Jam’iyyar APC tuni suka bayyana a shafukan Intanet.

Idan za a iya tunawa an nada Bello mai tallafa wa Sanata Uba Sani kan harkokin majalisa a shekarar 2019.

Kuma saboda hango burin Bello ne dan majalisar da ke wakiltar Kaduna ta Arewa, Alhaji Sama’ila Suleiman ya koma jam’iyyar hamayya ta PDP.

Sauran ’ya’ya da ’yan uwan manyan ’yan siyasa da ke son tsayawa takara

Musa Halilu: Musa Halilu Dujiman Adamawa dan uwa ne ga Uwargidan Shugaban Kasa, Ai’sha Buhari, wanda yake sha’awar tsayawa takarar Gwamnan Jihar Adamawa. A zaben shekarar 2019 ma ya tsaya takarar a Jam’iyyar APC.

Abba Kabir wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida fitacce a siyasar Kano. Sai dai ana ganin ko rashin nasararsa a zaben 2019 ba ya rasa nasaba da alakar da ke tsakaninsa da Sanata Kwankwanso ta surkuntaka. A zaben 2023 Abba zai yi takara ne a Jam’iyyar NNPP.

Godswill Edward: Goodswil ma surukin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ne da ke neman takarar Gwamnan Jihar Kuros Riba.

Edward wanda Mai ba Gwamna Ben Ayade Shawara ne a kan Wasanni da Fim, zai yi takara ne a Jami’iyyar APC.

Marilyn Okowa Daramola: Marilyn ’yar Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa ne da ke son tsayawa takarar Majalisar Jiha don wakiltar mazabar Ika North East.

Misis Ebelechukwu Obiano: Matar tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano an ce tana son tsayawa takarar Sanata don wakiltar Anambra ta Arewa.

Sanata Abdul’aziz Nyako: Sanata Nyako tsohon sanata ne da ya wakilci Adamawa ta Tsakiya. A zaben 2019, ya yi takarar Gwamnan Jihar Adamawa a Jam’iyyar ADC. Tsohon Sanatan yanzu ya koma APC, inda yake son sake takarar Sanata domin komawa kujerarsa.

Bai dace a mayar da dimokuradiyya kamar sarauta ba – CISLAC

Da yake bayyana ra’ayinsa kan wannan hali da ake ciki, Babban Daraktan Kungiyar Kare Hakkin Jama’a da Samar da Shugabanci Nagari ta CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya yi gargadin cewa bai kamata ’yan siyasa su mayar da dimokuradiyya kamar tsarin sarauta ba.

Ya ce, yanayin da gwamnoni da tsofaffin gwamnoni ke ingiza ’ya’yansu wadanda watakila ba su da gogewar siyasa da karfin da za su iya rike mukaman siyasa, hakan na iya haifar da tsoma-baki da rashin iya shugabanci. “Wannan dabi’a ta ’yan siyasa wadanda har yanzu suke kan mukamansu ko suka bar mukaman suna kokarin ganin sun tsoma ’ya’yansu da ’yan uwansu a harkokin mulki, wadansu ’ya’yan ko dangi ba a ma san su a harkar siyasa ba, kawai suna samu alfarmar siyasa ce tare da tsoma hannunwansu a taskar gwamnati, wannan abin damuwa ne.

“Yanzu suna tabbatar da cewa, ba tare da goyon bayan jama’a masu zabe ba, za su iya amfani da tasirinsu wajen dora danginsu. Hakika wannan ba ci abu ne mai kyau ba, domin ba a kan goyon bayan jama’a ko cancantar dimokuradiyya ba ne, ko kwarewa a harkokinsu na siyasa ko rayuwa.

“Duk da cewa ba ma jayayya cewa ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da alakarsu da daidaikun mutane ba, sun cancanci tsayawa takarar mukaman siyasa, amma idan aka yi haka don tura dangi su ci gajiyar siyasa don kare bukatun siyasa, a ci gaba da samun damar yin rub-da-ciki a kan baitul malin jama’a a ci gaba da nuna isa wannan ya zama abin damuwa.

“Ina ganin ya kamata ’yan siyasa su yi taka-tsantsan, domin hakan zai zama tauye dimokaradiyyar wadansu ’yan Najeriya wadanda saboda ba su da ubangidan siyasa da suka tara makudan kudaden da za su biya ga jam’iyyun siyasa ko jami’an zabe da na tsaro, an hana su shiga a fafata da su. Wannan ba abu ne mai kyau ba, domin zai nisantar da jama’a daga shiga harkokin siyasa don irin wadannan mutane za su ci gaba da yin magudin zabe da kuma yin karan-tsaye a harkokin siyasa,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Wannan shi ya sa za mu ci gaba da fama da rashin shugabanci nagari, saboda ba su da kwarewa wajen tafiyar da al’amuran jama’a. Gudanar da al’amuran jama’a ba abu ne na gado ba; batun shi ne a sa mutane masu gaskiya da kwarewa da kuma tabbatar da masu tarihi wajen bayar da shawarar adalci na zamantakewa ciki har da tabbatar da cewa, an san mutanen da ke neman mukaman.

“Idan masu takarar ba su da wadannan halaye kuma kawai abin da ake bukata shi ne mahaifinsa ko ya kasance minista ko gwamna ko shugaban siyasa, ina ganin hakan bai dace ba ga ’yan Najeriya, saboda sake amfani da su yana daidai da yin tsarin da iyayen gidansu suka yi ne.

“Yana da muhimmanci ’yan siyasa su yi taka-tsantsan su mutunta hazakar ’yan Najeriya. Har ila yau, ba muna musunta cewa, wadannan mutane suna da hakki ba ne, amma ya kamata a yi la’akari a cikin wannan saboda da zarar ka zama Gwamna, kana da tasiri mai yawa kuma kana iya yin amfani da tsarin ka sauya yadda kake so. Shi ya sa muke bukatar mu yi taka-tsantsan.

“Za mu zo wani yanayi da za mu koma salon sarauta ba dimokuradiyya ba; kuma hakan zai shafi shiga harkokin siyasa. Kada mu mayar da mulkin dimokuradiyya na sarauta, inda dangi ne kawai za su ci gaba da gadon mulkin siyasa kamar yadda yake faruwa a tsarin gargajiya. Ba ma son haka ya faru. Hakan zai gurgunta mutunci, kwarewa da kishin kasa a harkokin mulki,” inji shi.

Daga: Itodo Daniel Sule da Ahmed Mohammed, Bauchi da Salihu Makera da Isyaku Muhammed da Jamilu Adamu