Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce yawon kiwon dabbobi ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.
Masari ya bayyana hakan ne a tsokacinsa kan batun haramta yawon kiwo da gwamnonin Kudu suka yi, ake kuma ta mahawara a kai a Najeriya.
“A ganinmu yawon kiwo ba Musulunci ba ne kuma ba shi ba ne mafi a’ala. Yana daga cikin matsalolin da muke fuskanta a yanzu saboda haka ba na goyon bayan a ci gaba da yawon kiwo,” inji shi.
Gwamnan Katsinan ya bayyana hakan ne a ofishinsa lokacin taron cikarsa shekara biyu a wa’adin mulkinsa na biyu a Jihar.
Masari ya jaddada muhimmancin samar wadatattun abubuwan da ake bukata domin hana yawon kiwo daga wani yanki zuwa wani da sunan neman abincin dabbobi.
“Me ya sa makiyaya ke tashi daga Katsina su je wani wuri? Abu biyu ne: ruwa da ciyawa. Idan muka samar da su, to me zai sa su rika tashi?”
Ya kuma ce yana goyon baya 100% a yi rabon iko tsakanin matakan gwamnati uku, wanda ya ce shi ake nufi da sauya fasalin kasa.
Masari ya ce ya kamata idan aka tashi yin hakan Gwamnatin Tarayya ta sanya mizani ko iyaka wanda ba za a ketara ba.
A cewarsa, a yayin da Jihar Legas ke samun kudaden shiga Naira biliyan 400, abin da Jiharsa ke samu bai wuci biliyan biyu ba.
“Saboda haka idan aka yi rabon ikon yadda ya dace, ko aka sauya fasalin kasar, na san dole abin da Gwamnan Kano zai samu (na kudaden shiga) zai fi nawa. Shi kuma Kansila a Jihata, abin da zai samu zai kasance ne gwargwadon karfin arzikin jihar.
“Maganar sauya fasalin kasa an dade ana yin ta, tun a Jamhuriya ta Daya. An tattare karfin iko da yawa a tsakiya; Ba na tunanin akwai mai son a dore a hakan,” inji Masari.