✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kashe mutane 28 a sace 24 kullum a Najeriya —Rahoto

Adadin mutanen da ake kashewa ya zarce wadanda aka yi garkuwa da su, cewar wani sabon rahoto kan sha'anin tsaro a Najeriya

Wani sabon rahoto kan sha’anin tsaro a Najeriya ya nuna yawan mutanen da ake kashewa a kullum a kasar ya zarce na waɗanda ake yin garkuwa da su, kuma abin ya fi muni a yankin Arewa.

Rahoton ya nuna a kullum ana kashe akalla mutane 28, ana yin garkuwa da 2,164 a tsawon watanni uku na farkon 2024 a kasar.

Rahoton, wanda kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, — masu bincike kan hatsarin rashin tsaro — ya fitar, ya bayyana cewa kashe-kashe da sace-sace an fi yin su ne a jihohin Arewa Najeriya.

Ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Maris,  kaso 80 cikin 100 na kashe-kashen da kuma kashi 94 cikin 100 na sace-sacen an yi su ne a jihohin Arewa.

Rahoton ya nuna ana kashe mutane 28 kullum a Najeriya, ana garkuwa da 24.

Sai dai wannan rahoto ya ci karo da ikirarin da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya yi na cewa, matsalar tana raguwa kwarai da gaske.

Shi ma dai Ministan Harkokin Tsaron Najeriya Muhammad Badaru Abubakar a farkon watan nan yayin wani taro na rundunar sojojin kasar nan ya bayyana cewa ana samun cigaba wurin yakin da ta’addanci a Najeriya.

Alkaluman kashe-kashe

Alkaluman sun nuna daga cikin mutanen da aka kashe a wata ukun farkon 2024, 793 sun fito ne daga yank Arewa maso Yamma, 681 daga Arewa maso Gabas, sai 596 daga Arewa ta Tsakiya.

Wannan ya haɗa da hare-haren ’yan bindiga, rikicin manoma da makiyaya da kuma rikicin kabilanci.

A Kudu-maso-Yamma kuma an kashe mutane 194, a Kudu-maso-Kudu mutane 161, Kudu-maso-Gabas kuma 158.

Sai dai kuma a yankin aka fi samun rahotannin garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

Inda abin ya fi ƙamari

Jihohin biyar da aka fi kashe-kashe su ne Borno 517, Binuwai  313, Katsina 252, Zamfara 212, sai kuma 206 Kaduna 206.

Alƙaluman Garkuwa Da Mutane

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutane 2,164 da aka sace a cikin watanni uku na farkon 2024, an yi garkuwa da 1,297 a Arewa maso Yamma.

An sace mutane 421 a Arewa maso Gabas, sai 330na Arewa ta Tsakiya.

A kudu maso Yamma kuma an dauke mutane 30, Kudu maso Kudu, 66 sai kudu maso Gabas mutane 20.

Jihar Kaduna ta fi ko’ina yawan mutanen da aka sace da mutane 546 a watanni uku na farkon 2024.

Sai Jihar Zamfara, in da aka sace mutane 447.

An fi kashe mutane a Jihar Borno, amma kuma ita ce ta uku wajen satar mutane, da mutum 340.

Sai Jihar Katsina, inda aka ɗauke 252 sannan Babban Birnin Tarayya Abuja, inda a watanni ukun farkon 2024 aka yi garkuwa 102 domin neman kudin fansa.

Akwai Alamun nasara

Sai dai duk da haka, masu sharhi a kan harkokin tsaro suna bayyana cewa akwai alamun nasara a yunƙurin dakile wannan matsala da ke neman gagarar kundila.

Ahmed Getso, ya bayyana cewa, yadda jami’an tsaro suka kara kaimi wurin fatattakar ’yan bindiga ya sa masu aikata laifuka yin hijirar dole, zuwa sabbin wuraren ta’addanci don gujewa jami’an tsaro.

“Tunda jami’an tsaro suka mayar da hankali kan ayyukansu a wuraren da ke da hadari, masu aikata laifuka kan yi kaura zuwa yankuna daban-daban,”

Ya ce, wannan gwamnatin tana sauraron shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar.

Shugaban kamfanin tuntuba kan harkokin tsaro, Beacon Consultants, Kabiru Adamu, a hirarsa da Aminiya ya danganta matsalar tsaro a Arewa da rashin ingantaccen tsarin shari’a da rashin kula da iyakoki da kuma  yaduwar kananan makamai ta ba bisa ka’ida ba.

Ya ce, dimbin matasan da ba su da ilimi ko kuma sanin makamar wani aiki, da kuma tsarin shugabanci na kasa biyan bukatun cigaban al’umma suna haifar da babban kalubale.

Adamu ya ce, za a iya shawo kan matsalolin tsaron kasar nan ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin tsaro, gwamnatin tarayya da  jihohi da kuma kasashe makwabta.