✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yawan Amurkawan da ke neman ‘tallafin zaman kashe wando’ ya karu sosai

Sashen da ke kula da kwadago na Amurka a ranar Alhamis ya rawaito cewa masu neman tallafin rashin aikin yi daga gwamnati ya karu daga…

Sashen da ke kula da kwadago na Amurka a ranar Alhamis ya rawaito cewa masu neman tallafin rashin aikin yi daga gwamnati ya karu daga 1,000 zuwa 203,000 a sati guda.

A makon da ya gabata dai wata dayan da kasar ke bayarwa na cike gurbi domin zuwa karbar tallafin ya karu daga mutane 4,250 zuwa 192,750.

A satin da ya kare ranar 30 ga watan Afrilun 2022 kuwa, adadin mutane ya karu daga 44,000 zuwa 1,343,000, wanda shine mafi kankantar adadi da aka samu a Amurka tun ranar uku ga watan Junairun 1970.

Yan kasar dai na morar aikin shekaru biyu kwarara tun bayan bullar annobar COVID-19 da ta jefa tattalin arzikin kasar a mawuyacin hali.

Gwamnatin Amurka ta rawaito ma’aikatanta sun kara ayyuka 428,00 kari kan wanda suke yi a watan Afrilun, wanda hakan ke nuna adadin marasa aikin ya kai kaso uku da digo shida.

A farkon watan Mayun 2022 ne sashen kwadago da kididdiga na Amurkan ya ba da rahoton kididdigar cewa a watan Maris kadai masu daukar aiki a kasar sun ba da sanarwar daukar aiki miliyan 11.5.

Kazalika, ta rawaito ’yan kasar miliyan 4.5 da suka ajiye aiki a watan na Maris din kadai, bisa tunanin za su samu aikin da ya fi wanda suke yi.