✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaushe za a fara samun mata masu bayar da umarni a Kannywood?

A harkar fim, mata sun fi suna da samun daukaka a bangaren fim, wato zama jarumai.

A harkar fim, mata sun fi suna da samun daukaka a bangaren fim, wato zama jarumai.

Ko a Kannywood, idan aka cire irin su Ali Nuhu da Sani Danja da Adam A. Zango, jarumai mata irin su Rahama Sadau da Nafisat Abdullahi da Hadiza Gabon sun samu daukaka cikin kankanin lokacin da suka shigo masana’antar.

Haka kuma ana ganin kamar jarumai matan sun fi arziki da abin duniya, musamman yadda ake ganin suna watayawa a kasashen duniya, yayin da wasu mazan da dama da suka dade a masana’antar suke komawa Allah-ba-ku-mu-samu da zarar sun fara tsufa, harkar ta daina yi da su.

An sha ganin tsofaffin jarumai maza suna galabaita bayan fim ya daina yi da su, duk da cewa akwai wasu tsofaffin jaruman mata su ma da suke samun irin wannan koma bayan da karyewar arziki.

Sai dai duk da haka, akwai bangaren da jarumai matan ba su cika shiga ba, wato bangaren bayar da umarni.

A masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood, an samu zaratan masu bayar da umarni da suka yi shuhura.

Akwai irin su Mo Abudu, mai Kamfanin Ebonyi Life wadda ta shirya ta kuma bayar da umarni a wasu manyan finafinan Kudu.

Daga cikin finafinanta akwai ‘Blood sisters’ da ya samu makallata sama da miliyan 11 a manhajar Netflix a cikin awanni kadan da fitar da shi.

Ita ma Kemi Adetiba fitacciyar darakta ce a masana’antar shirya fim ta Kudu. Daga cikin finafinanta akwai irin su King of Boys da Wedding Party da sauransu.

Idan aka dawo bangaren shirya finafinai kuwa, jarumai mata na Kudu su ne kan gaba wajen shirya finafinai da suka samar da kudade.

Aminiya ta ruwaito cewa, fim din Funke Akindele mai suna Battle on Buka Street shi ne fim wanda ya fi samar da kudi, inda ya samar da Naira miliyan 668,423,056.

Haka kuma fim din Omo Ghetto: The sage, wanda shi ma Funke din ce ta shirya ne na biyu wajen samar da kudi, inda ya samar da Naira miliyan 636,129,120.

Ke nan duka finafinanta guda biyun sun samar da sama da Naira miliyan 600.

Wedding Party na Kemi Adiba ne na uku a wajen samar da kudi, inda ya samar da Naira 452,288,605.

Ke nan mata da dama suna jan ragamar harkokin fim a Kudancin Nijeriya a bangaren shirya fim din da ma bangaren bayar da umarni.

A Masana’antar Kannywood, an samu mata da suka shirya finafinai da dama da suka yi shuhura.

Rahama Sadau ta shirya finafinai manya, irin su Mati a Zazzau da ya yi tashe a sinima.

Haka ita ma Nafisat Abdullahi ta shirya fim din Yaki A Soyayya wanda shi ma ya yi tashe matuka.

Yanzu haka jaruma A’ishatu Humaira ta shirya tsaf domin fara daukar shirinta na A Cikin Biyu, wanda ya kunshi manyan jarumai irin su Ali Nuhu da Adam A. Zango da sauransu.

Haka akwai finafinai da dama da jarumai mata irin su Hannatu Bashir da sauran jarumai mata suke shiryawa.

Akwai ma finafinan da wasu matan, wadanda ba jarumai ba ne suke shiryawa, inda su a masana’antar suka kasancewa kawai masu shirya finafinai, ba masu fitowa a ciki ba.

Amma binciken Aminiya ya gano cewa, har yanzu ba a samu cikakkiyar darakta ba a masana’antar ta Kannyood, inda jaruma za ta bayar da umarnin fim cikakke.

A shekarar 2020 ce ya kamata jaruma Nafisat Abdullahi ta bayar da umarnin fim dinta mai suna Zainab Ali a kamfaninta mai suna Nafs Entertainment, amma hakan bai yiwu ba saboda yanayin yadda duniyar ta shiga rudu a lokacin na annobar Kwarona.

Wadansu na ganin bayar da umarni aiki na maza, domin yana bukatar juriya da karfin hali.

Sai dai Aminiya ta gano cewa, tsohuwar jaruma Muhibbat Abdulsalam, wadda matar darakta Hassan Giggs ta taba zama mai bayar da umarni a Kannywood.

Sai dai duk da haka, wasu suna tunanin kawai an saka sunanta ne, kasancewar mijinta fitaccen darakta ne, don haka ya taya ta aikin, sai aka ga sunanta a matsayin wadda ta yi aikin.

Domin yin wannan aikin na bayar da umarni, Nafisat ta yi tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin karo ilimi da shirye-shirye.

A cikin dalilinta na ficewa daga shirin Labarina mai dogon zango na Aminu Saira, ta bayyana rashin isasshen lokaci da karatu da kuma fim dinta da take aiki a kai a matsayin wasu daga dalilanta na ficewa daga fim din.

Sai dai har yanzu ba a fara daukar fim din ba na Zainab Ali, wanda dama a shi ne aka yi zaton fara ganin ta tana bayar da umarni, wanda ake tunanin zai bude wani sabon babi a Masana’antar Kannywood, inda ta za zama zama cikakkiyar darakta a masana’antar ta Kannywood.