A ranar Talatar da ta gabata ce dan wasan Portugal da Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya ya kafa sabon tarihi a wasan tamola inda ya zama dan kwallo namiji na farko da ya buga wasa 200.
Haka kuma dan wasan ya jefa kwallo a wasan, inda ya kasance yana da kwallo 123, inda ya kara tserewa abokin hamayyarsa, Lionel Messi wanda yake da kwallo 103.
Kafin a fara wasan ne Kundin Adanan Tarihi na Duniya (Guinness World Record) ya mika masa kambin wannan tarihi da ya kafa.
A shekarar 2003 ce Ronaldo ya fara taka leda a a kungiyar kasar Portugal, inda yanzu ya kwashe kusan shekara 20 yana taka leda.
Kafin wasan, an tambaye shi ko yaushe zai yi ritaya?
Sai ya amsa da cewa yana matukar jin dadin wakiltar kasarsa ta Portugal a wasan kwallo, don haka ne yake tunanin da sauransa har yanzu, kuma zai ci gaba da taka ledar har zuwa wani lokaci nan gaba.
Dan wasan ne kadai a tarihi ya taba buga gasar Nahiyar Turai sau biyar, sannan yanzu haka yake shiryeshiryen zuwa karo na shida a badi.
Sannan a gasar Kofin Duniya na bara, dan wasan ya kafa tarihin zama dan wasan na farko da ya zura kwallo a gasannin Kofin Duniya guda biyar daban-daban.
Sannan ya lashe kofi biyu da kasarsa Portugal, wato Kofin Nahiyar Turai a shekarar 2016 da ta UEFA Nations League.
Sai dai duk da wannan tarihin da ya kafa a wasan maza, ana ganin zai yi wahalar gaske ya iya kamo ’yar wasan da ta fi buga wasanni a kwallon mata.
Kristine Lilly, ’yar wasan kwallon kasar Amurka ce ta fi buga wasanni a kwallon kafa na mata, inda ta taka leda a wasa 354.
A farkon kakar bara ce aka yi tunanin ko ta kare wa dan wasan ne, inda bayan ya raba gari da Kungiyar Manchester United ya rasa kungiyar da zai je domin ya ci gaba da tala leda a Gasar Zakarun Turai, inda aka fafata gasar ba tare da shi ba, duk da cewa shi ne ya fi zura kwallaye a gasar.
Dan wasan, wanda ya lashe Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Duniya sau biyar, manajansa na wancan lokacin, Jorge Mendes ya yi ta kokarin nema masa wata kungiyar da zai ta fafata a gasar, amma hakan bai samu ba domin ba a samu wata babbar kungiya da ta taya dan wasan ba.
An yi ta tirka-tirka a tsakanin dan wasan da Manchester United, wadda ta ce ba za ta bar dan wasan ya tafi ba, shi kuma ya dage sai ya tafi, wanda hakan ya sa bai samu halartar atisayen kungiyar ba kafin a fara kakar bara.
Sai dai duk da wannan matsala da aka samu, a kakar wasanninsa na karshe, dan wasan gaban ne ya fi zura kwallaye a Manchester United inda ya ci kwallo 24 a wasa 37 da ya buga wa kungiyar.
Bayan ya tafi gasar Kofin Duniya ta bara ce aka saki wata tattaunawa da ya yi, inda a ciki ya caccaki Kungiyar Manchester United, wanda dole suka samu maslaha wajen rabuwa da shi.
Sai dai kafin nan, an riga ajiye shi a benci a wasannin kungiyar, inda kocin kungiyar, ya fi amfani da Rashford da Sancho da sauransu.
Hakan ya sa a lokacin aka yi zaton dan wasan ya yi kwantai ne domin ba a yi tsammanin za a iya rasa babbar kungiyar da za dauki dan wasan ba.
A lokacin ne Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya ta taya dan wasan a sama da Fam miliyan 200, wanda da ya amsa ya zama wanda ya fi kowane dan kwallo karbar albashi da kusan ninkin albashin Mbappe.
Kungiyar ta sa wa dan wasan Fam miliyan 2.24 a matsayin albashinsa na mako, inda ta dauke shi domin ya taka leda a kungiyar na shekara biyu.
Gasar Kwallon Saudiyya na kara samun tagomashi
A farkon bana ne dan wasan kasar Faransa da Kungiyar Chelsea Kante ya amince da yarjejeniyar tafiya Kungiyar Al Ittihad ta Saudiyya domin ci gaba da taka leda.
Dan wasan zai hadu da abokinsa, Karim Benzema ne a kungiyar, bayan Gwarzon Kwallon Duniya na yanzu shi ma ya sanya hannu a kwantiragin shekara hudu a kungiyar.
Kante zai samu Fam miliyan 100 baya ga alawus-alawus na shekara hudu.
Al Ittihad ce ta lashe Gasar Saudiyya ta bara, sannan ta kara zaratan ’yan wasa, kuma yanzu haka tana ci gaba da neman wasu zaratan ’yan wasan daga Turai.
Ita kuma Kungiyar Al Nassr ta Ronaldo ta kusa dauko dan wasan Chelsea Hakim Ziyech.
Sauran zaratan ’yan wasan da ake tunanin za su tafi Saudiyya su ne Kalidou Koulibaly da Edourd Mendy da sauransu.