A daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ranar Litinin za ta bude shafin rijistar tallafinta na kanana da matsakaita sana’o’i, an fitar da jadawalin rukunin sana’o’in da za su ci gajiyar.
Tallafin dai wanda aka yi wa lakabi da Survival Funds, an kirkiro shi ne da nufin tallafa wa masu karamin karfi da kuma kananan sana’o’i domin su samu su farfado daga masassarar annobar COVID-19.
Sanarwar da ofishin kula da shirin ya fitar ranar Lahadi ta ce za a bude shafin ne daga karfe 10 na daren ranar Litinin, 21 ga watan Satumba kuma makarantu su ne farkon rukunin da za su yi rajista domin cin gajiyar shirin.
A cewar sanarwar, “Mun tsara yin jadawalin ne saboda masu sha’awar yin rajista domin amfana da shirin su yi haka ba tare da shan wahala ba.
“Za a fara da makarantu ranar Litinin, sai kuma sana’o’in da su ke bangaren harkar bude ido da za su fara ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba da misalin 12 na dare.
“Za a bude shafin ga sauran masu wasu sana’o’in a ranar Litinin mai zuwa da 12 na daren ranar Litinin, 28 ga watan Satumbar 2020”, inji sanarwar.
Daga nan sai ofishin ya shawarci masu sha’awar yin rajistar da su lura da ranakun da aka tsara a cikin jadawalin da kuma ziyartar shafin http://www.survivalfund.ng domin fara yin rajistar.