A Laraba za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali a aikin Hajjin bana.
Jirgin sahun farkon zai tashi ne a Kebbi da maniyyatan jihar, kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar.
Kimanin maniyyata 65,000 ne ake sa ran za su sauke farali daga Najeriya a aikin Hajjin bana.
Hukumar ta ce ana sa ran tashin jiragen maniyyata biyu a kullum daga filayen jiragen sama 15 da aka ware a fadin Najeriya, har sai an kammala kai su Kasa Mai Tsarki.
- Kuncin Rayuwa: Kungiyar Izala Ta Ba Da Umarnin Fara Alkunut
- Yadda Aka Kashe Babban Aminin Shekau, Tahir Baga
NAHCON ta bayyana cewa tana sa ran kammala kwashe maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya kafin ko a ranar 10nga watan Yuni, 2024.
Aminiya ta ruwaito shugaban NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, yana cewa maniyyatan za su shafe akalla kwanaki hudu a birnin Madina domin yin ziyara kafin su wuce Makkah domin yin Umrah da aikin Hajji.
A ranar Laraba 14 ko Alhamis 15 ga watan Yuni ake sa ran fara aikin Hajjin 2024, inda za a yi Hawan Arafa a washegari.
Alhazai za su yi Hadaya da jifan farko hadi da Babbar Sallah a washegari.