✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a ci gaba da gasar cin kofin zakarun Turai

A yau Talata za a ci gaba da buga wasannin gasar cin kofin Zakarn Turai a matakin gab da na biyun karshe, inda kungiyoyin da…

A yau Talata za a ci gaba da buga wasannin gasar cin kofin Zakarn Turai a matakin gab da na biyun karshe, inda kungiyoyin da suka yi nasara a zagayen ’yan 16 za su yi fito-na-fito a tsakaninsu.

Wasan da za a fafata yau za a kara ne tsakanin Real Madrid da Liverpool, inda magoya bayan kungiyoyin biyu ke fatan samun nasara.

Za a maimata haduwar ne tsakanin kungiyoyin biyu kamar yadda haduwarsu tare ta kasance a wasan karshe na gasar shekaru uku da suka gabata wanda Real Madrid ta yi nasara.

Magoya bayan Liverpool sun zira idanu don ganin kungiyar ta rama abin da Real Madrid ta yi musu na haramiyar cin kofin a wancan lokaci.

Sai dai mai horar da ’yan wasan Liverpool, Jurgen Kloop, ya ce ba za su tunkari Real Madrid a yau ba da zummar ramuwar gayya, amma ko shakka babu suna fatan samun nasara a kanta.

A wancan lokaci, Real Madrid ta lallasa Liverpool da kwallaye 3-1 a lokacin da tauraron dan wasa, Cristiano Ronaldo yana kan sharafinsa a kungiyar.

A yanzu da babu shi, da dama daga cikin masoya kwallon kafa na ganin Real Madrid tana da wani nakasu wanda babu lallai ta yi nasara kasancewar Liverpool ta tara gwanayen ’yan kwallo masu jini a jika.

A wani bangaren kuma na gasar cin kofin Zakarun Turan, za a yi gumurzu tsakanin Manchester City da Borrusia Dortmund a filin wasa na Etihad da ke Ingila.

Babu shakka yadda tauraruwar dan wasan Dortmund Erling Halaand ke haskawa, za ta sanya kocin Manchester City, Pep Guardiola ya yi wa yaransa karatun ta nutsu dangane da hatsarin dan wasan.

A baya bayan ne Pep Guardiola ya jinjinawa Haalanda kan kokarin da yake a yanzu a tamaula, inda dan wasan mai shekara 20 shi ne kan gaba a yawan kwallaye a gasar cin Zakarun Turai na bana da kwallaye 10 a raga.

A yayin da a makon jiya ne Manchester City ta sanar da cewa dan wasan gabanta, Sergio Aguero, zai yi bankwana da ita a karshen kakar wasanni a bana, ana ci gaba da alakanat Haalanda a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai manema labarun wasanni da dama sun ruwaito Guardiola yana cewa, farashin da aka sanya wa dan wasan na Euro miliyan 150 ya yi tsada, kuma Manchester City ba ta iya biyan abin da ya zarta Euro miliyan 100 kan dan wasa guda ba.