Yau Talata Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai rantsar da kwamitin karin mafi karancin albashi na kasa.
Za a kaddamar da kwamitin ne sakamakon tashin gwauron zabon kayan masarufi da ya biyo bayan janye tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta yi.
Kwamitin wanda ke da wakilai da ga bangaren gwamnati da ’yan kwadago da kamfanoni masu zaman kansu da sauransu zai tattauna ya ba da shawara kan sabon mafi karancin albashin da kuma yadda za a fara biya.
A watan Afrilun 2019 ne gwamnatin Najeriya ta yi karin mafi karancin albashi na karshe, daga N18,000 zuwa N30,000.
- Yadda aka yi wa mutane 600 auren gata a Kebbi
- Yadda Tsadar Rayuwa Ta Sa Aka Koma Hawa Jaki A Arewa, Kudu Kuma Tafiyar Ƙafa
A watan Afrilun 2023 kuma Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bukaci gwamnatin ta kara mafi karancin albashin zuwa akalla N200,000.
NLC ta bukaci hakan ne sakamakon tsadar rayuwa da ta biyo bayan janye tallafin mai da Tinubu ya yi.
Bayan zanga-zanga da bore da NLC ta jagoranta kan matsin rayuwa da al’ummar kasar suka shiga, a jawabin Tinubu na Zagayowar Ranar Samun ’Yancin Najeriya, 1 ga Oktoba, 2023, ya yi alkawarin kara mafi karancin albashi daidai da halin da kasar ke ciki.
Amma kafin nan ya nasar da karin N35,000 a kan albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na tsawon watanni shida, a matsayin matakin wucin gadi; ko da yake kawo yanzu dai ana ta kai ruwa rana kan biyan N35,000 din.
A lokacin ne kuma ya sanar da ba da tallafin Naira biliyan biyar da suka hada da hatsi ga kowacce daga gwamnatocin jihohi domin raba wa al’ummominsu.
Haka kuma ya sanar da shirin samar da motocin sufuri masu sauki, da kuma shirin sarrafa ababen hawa masu amfani da fetur su koma amfani da iskar gas da sauransu.