Al’ummar Jihar Anambra sun fara fita don kada kuri’unsu a zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa yayin da a wasu wurare jami’ai da kayan zabe suka isa a kan lokaci, a wasu wurare an samu jinkiri.
- Najeriya A Yau: Yadda ake ciki kan zaben Gwamnan Anambra
- Yadda muka tsallake harin masu garkuwa sau 3 a rana daya
A wasu wurare kamar Karamar Hukumar Njikoka, sai kusan karfe8.00 na safe jami’ai da kayan aiki suka bar ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) zuwa cibiyoyin da ya kamata a kai su.
Masu sa ido na Shirin Yada Labaran Zabe na Cibiyar Binciken Kwakwaf ta Premium Times sun ruwaito jami’an suna shaida musu cewa sun makara ne saboda rashin zuwan kayan aikin a kan lokaci.
Duk da cewa IPOB ta janye barazanar hana gudanar da zaben dai, ana fargabar mutane ba za su fito sosai ba.
‘Babu gudu…’
Barazanar ta IPOB dai tun da farko ba ta hana INEC jaddada aniyarta cewa babu gudu babu ja da baya ba wajen gudanar da zaben na ranar Asabar.
Wakilin Daily Trust Abbas Jimoh ya ruwaito Shugaban Hukumar, Farfsa Mahmood Yakubu, yana fadar haka a wani sako da ya aike wa ma’aikatansa ranar Juma’a.
“Babu gudu ba ja da baya a kudurinmu na tabbatar da cewa an gudanar da wannan zabe kamar yadda aka tsara.
“Don haka ne muka gyara gine-ginenmu muka kuma sauya kayan aikinmu [wadanda aka lalata], sannan muka bukaci – muka kuma samu – tallafi da goyon baya daga jami’an tsaro, da jam’iyyun siyasa, da ’yan Takara da sauran masu ruwa da tsaki.
“Mun kuma aika da dukkan kayan zabe a kan lokaci, mun tura jami’an zabe, sannan mun tanadi dukkan abubuwan da ake bukata don kai kayan aiki da ma’aikata zuwa dubban wurare a Jihar Anambra…”, inji Farfesa Yakubu.
Jam’iyyun da ke fafatawa
APGA ce jam’iyya mafi girma a Jihar kuma ta shafe shekara 19 tana mulkin Anambra, tun daga 2005.
Ana ganin hakan a matsayin kalubale ga jam’iyyun siyasa mafiya girma a Najeriya, wato APC mai mulki da kuma PDP, kasancewar ba su suke mulkin Jihar ba.
Ana iya tuna cewa a ranar 23 ga watan Yuni ne aka bayyana tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Charles Soludo a matsayin ɗan takarar APGA kuma Gwamna Willie Obiano ya ba shi tutar takara ranar 25 ga Satumba.
Hakan na nufin zai fafata da Valentine Ozigbo na Jam’iyyar PDP da Andy Uba na Jam’iyyar APC.
Kazalika, akwai wasu da ake ganin za su taka rawar gani a zaben kamar Obiora Okonkwo na ZLP, da Ifeanyi Uba na YPP.
’Yan sanda 34,500
Jiragen yaki uku da ’yan sanda 34,587 aka ce za a tanada domin tabbatar da tsaro yayin zaben na Jihar Anambra.
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ne ya ba da umarnin tura su tun a watan Oktoban da ya gabata.
Ya ce ’yan sandan da za a tura sun hada da jami’ai na musamman da sauransu don tabbatar da isasshen tsaro a jihar duba da yadda ’yan kungiyar awaren Biafra ta IPOB take neman tayar da zaune tsaye yayin zaben.
Baba ya kuma ce an tura jiragen yaki uku zuwa jihar ta Anambra domin yin shawagi a lokacin zaben.
Kazalika, ya ce za a tura horarrun dabobbi wadanda za su taimaka wa jami’an da aka tura wajen dakile duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye ko kuma hana gudanar zabe cikin lumana.
“Muna ci gaba da hada gwiwa da INEC don ganin an gudanar da sahihin zabe kuma cikin lumana.
“Don haka mun aike da jami’an tsaro domin tabbatar da ganin an samu cikakkacen tsaro, tare da dakile duk wata barazana a lokacin zaben,” inji Sufeto Janar din.
Har wa yau, ya ce duk kwamandan da ya kasa aiwatar da aikin da aka ba shi kamar yadda ya ba da umarni za a hukunta shi.
Rahotanni sun bayyana cewa ita ma kungiyar MASSOB mai fafutikar kafa kasar Biafra ta ce babu wanda ya isa ya hana gudanar da zaben na ranar Asabar.
Babu bizar shiga Amurka
Kasar Amurka ta yi barazanar hana izinin shiga cikinta (biza) ga duk wanda ya yi kokarin ta da zaune tsaye a zaben Gwamnan Jihar Anambra na ranar Asabar.
Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya ya fitar a Abuja ranar Laraba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Amurka na fatan ganin an yi zaben Gwamna a Jihar Anambra ranar 6 ga watan Nuwamba lami lafiya, cikin adalci sannan sakamakonsa ya yi daidai da muradun ’yan Jihar.
“Za mu sanya ido sosai kan mutanen da za su yi yunkurin katsa-landan ga harkokin Dimokuradiyya, ko su ta da rikici kafin zabe, ko yayin zabe ko kuma bayan kammala shi.
“Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen daukar tsauraran matakai, ciki har da na hana bayar da biza ga duk wanda muka gano yana da hannu a kokarin kawo rikici.
“A karkashin dokokin shige da fice na Amurka, akwai laifukan da za su kai ga hatta iyalan mutum su ma a hana su.
“Muna kira ga ’yan kasa, malaman zabe da jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an yi ingantaccen zabe,” inji sanarwar.