✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau take ranar raba gardamar Zaben Gwamnoni 5 a Kotun Ƙoli 

Yau gwamnonin jihohin Kebbi, Nasarawa, Gombe, Delta da Ogun za su san makomarsu.

A wannan Juma’ar ce Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan Zaɓen Gwamnan Jihar Nasarawa da wasu jihohi huɗu.

Sauran jihohin da kotun za ta yanke hukuncinsu a yau sun haɗar da Ogun da Kebbi da Gombe da kuma Jihar Delta.

A watan Oktoba ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen Jihar Nassarawa ta soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.

To sai dai a watan Nuwamba kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen, inda ta mayar wa Gwamna Abdullahi Sule nasara kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana a lokacin zaɓen gwamnan jihar na 2023.

Tun farko INEC a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri’a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri’a 283,016.

A Jihar Gombe kuwa, jam’iyyar PDP da dan takararta, Mohammed Barde, suna fatan Kotun Ƙolin ta yi watsi da hukunce-hukuncen da kotun daukaka kara da kotun sauraron kararrakin Zaben suka yanke kan Zaben Gwamnan jihar.

Duk kotunan baya sun yi watsi da karar da suka shigar wajen kalubalantar nasarar da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana wa Gwamna Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a jihar ranar 18 ga Maris, 2023.

Kwamitin alkalan mai mutum biyar na Kotun Ƙolin karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ya yi na’am da hukunce-hukuncen zaben da aka yi domin yanke hukunci bayan dukkanin bangarorin sun amince da takaitaccen bayani.

A halin da ake ciki, kotun ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar ADC, Nafiu Bala ya shigar kan yana kalubalantar nasarar Gwamna Inuwa Yahaya.

Sai dai dan takarar ya janye karar ne bayan da kwamitin Kotun Ƙolin ya ja hankali kan cewa shari’ar na kunshe da hurumin da ya shafi batutuwan da za a iya saurara kafin zaben.

A bangaren Kebbi, kotun za ta yanke hukunci kan kararraki uku da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamna na 2023, Aminu Bande ya shigar yana kalubalantar nasarar Gwamna Nasir Idris na jam’iyyar APC.

Ana iya tuna cewa dai, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin da Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Kebbi ta yanke wanda a ranar 5 ga Oktoba, 2023 ta tabbatar da Idris a matsayin zababben gwamna.

Da farko dai INEC ta bayyana Zaben Gwamnan Jihar Kebbi da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon soke kuri’u da aringizon kuri’un da aka kada a kananan hukumomi 20 daga cikin 21 na jihar.

Daga baya hukumar ta tsayar da ranar 15 ga watan Afrilu domin gudanar da wani zabe.

Bayan sake zaben ne, Idris na APC ya samu kuri’u 409,225 inda ya doke Bande wanda ya samu kuri’u 360,940.

Sai dai Bande da jam’iyyarsa sun yi watsi da sakamakon, inda suka shigar da kara a gaban kotun.

A cikin ƙunshin korafin da suka gabatar, masu shigar da kara sun yi zargin cewa an yi aringizon kuri’u a wasu rumfunan zabe, kuma Gwamna Idris bai cancanci tsayawa takara ba.

Haka kuma, a wannan Juma’ar ce Kotun Ƙolin za ta yanke hukunci kan karar da Oladipupo Adebutu na jam’iyyar PDP ya shigar yana kalubalantar hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke wanda ya tabbatar da zaben Dapo Abiodun na jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Ogun.

Daga birnin Asaba na Jihar Delta kuma, Gwamna Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP zai san makomarsa dangane da kalubalantar nasararsa da jam’iyyar APC, LP da kuma SDP suke yi.

INEC dai ta bayyana cewa Oborevwori na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 360,234 inda ya lashe zaben gwamnan wanda ya doke Omo-Agege na APC, wanda ya samu kuri’u 240,229.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, kwamitin alkalai biyar na Kotun Ƙolin karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro, ya amince da karar da dukkanin bangarorin suka shigar bayan sun amince da bayanansu na karshe.

Hukuncin kotun daukaka kara a watan Nuwamba ya tabbatar da zaben Sheriff Oborevwori bayan alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a C.H. Ahuchaogu sun yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya shigar.

A halin yanzu, masu kara na fatan Kotun Ƙolin za ta soke hukuncin da kotun daukaka kara da ke Jihar Legas ta yanke a ranar 24 ga watan Nuwamba, wadda ta yi watsi da karar tasu saboda rashin cancanta, ta kuma tabbatar da Oborevwori na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.