Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar biyar ga watan Oktoban kowace shekara a matsayin Ranar Malamai ta Duniya.
Makasudin kebe ranar shi ne a yaba da aikin da malamai ke yi a kuma nemi hanyoyin magance matsalolinsu.
- ‘Yan China na yunkunrin kassara mana sana’a — ‘Yan Gwangwan
- Gwamnan Oyo ya ba masallatan Hausawa gudunmuwar motoci
Malamai suna da muhimmanci wajen kawo cigaban rayuwa, ba kawai don koyar da karatu da rubutu ba, har ma da koyar da kimiyya da fasaha da sauran bangarorin rayuwa.
Malam Isiyaka Abdullahi da ke garin Doma a Jihar Nasarawa, ya ce akwai karancin kayan aiki da rashin isassun malamai.
Haka kuma, Muryar Amurka ta ruwaito Kwamared Joshua Bala Bwede ya ce rashin biyan albashin malamai ya na dukufar da kuzarinsu na aiki.
Watanni takwas kenan tun bayan da malaman jami’o’i a Najeriya su ka shiga yajin aiki, har yanzu sun kasa daidaitawa da Gwamnatin Tarayya.
Dakta Peter Michael da ke jami’ar Modibbo Adama a Jihar Adamawa, ya ce tilas ne malamai su shiga yajin aiki don ayi gyara, amma a kullum gwamnati na cewa tana iyakar kokarinta.
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce ya zamo dole a sami ilimi mai inganci ta hanyar samar da kwararrun malamai.
Ko a bara sai da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da bai wa dalibai dake da niyyar zama malaman makaranta, tallafi na Naira dubu saba’in da biyar, yayin da wadanda ke kwalejojin Ilimi za su samu tallafin Naira dubu hamasin don ba su kwarin gwiwar samar da ilimi mai inganci.