A yau Juma’a 13 ga watan Nuwamba ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da Suwazilan a wasan sada zumunta. Wasan, wanda za a yi gida da waje, za a fara ne a filin wasa na Lobamba da ke Suwazilan sannan a ranar Talata mai zuwa 17 ga watan nan da muke ciki kuma a yi a filin wasa na Adokie Amiesiamaka da ke Fatakwal.
An shirya wasan ne a shirye-shiryen da Eaglets take yi na tunkarar gasar neman gurbi na hayewa gasar cin kofin Afirka da zai gudana a badi da kuma na cin kofin duniya.
Jami’in hulda da ’yan jaridu na kungiyar Mista Toyin Ibitoye ya ce tuni ’yan kwallon da aka gayyato suka halarci sansanin horar da su a Abuja inda suka zarce Suwizilan a jiya Alhamis.
’Yan kwallon da aka gayyato sun hada da Carl Ikeme da Dele Alampasu da yake kwallo a Fotugal da Ikechukwu Ezenwa na Sunshine Stars da ke Akure. Haka kuma akwai Chima Akas da ke buga wa kulob din Sharks na Fatakwal da kuma Austin Oboroakpo na kulob din Abia Warriors. Da alama mafi yawan ’yan kwallon da aka gayyata suna kwallo ne a gida.
Shi kuma mai kula da yadda al’amurra ke tafiya a kungiyar Mista Patric Pascal ya tabbatar cewa Koci Sunday Oliseh ne zai jagoranci kungiyar a wasan.
Shi dai Oliseh kimanin makwanni biyu ke nan rabon shi da Najeriya bayan an ba shi hutun makwanni biyu don ya tafi kasar waje a duba lafiyarsa. Ana sa ran zai zarce Suwazilan ne kai tsaye inda zai tarar da ’yan kwallon da zai jagorance su a wasan.
Yau Super Eagles za ta kece raini da Suwazilan
A yau Juma’a 13 ga watan Nuwamba ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da Suwazilan a wasan sada zumunta. Wasan,…