A yayin da Shugaba Bola Tinubu ke cika shekara 100 a kan mulki a yau din nan ne kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2023 za ta yanke hukunci kan shari’ar da ke kalubalantar nasararsa a zaben.
Kotun da ke zamanta a Abuja ta sahale wa kafofin yada labarai nuna zaman kai-tsaye, wanda ba kasafai aka saba yi ba.
- Kwana 100 na mulkin Tinubu a takaice
- DAGA LARABA: Me Ya Sa Tinubu Ya fi Damuwa Kan Juyin Mulki A Afirka?
Baban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu a zaben, tare da Peter Obi na jam’iyyar LP da ya zo na uku ne suka shigar a karar.
Atiku da Peter sun nuna kwarin gwiwar samun nasara a shari’ar, inda kowannensu ke neman kotun ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
A safiyar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023 ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar 25 watan da kuri’u mafi rinjaye — 8,794,726.
Tun kafin a kai ga sanar da sakamakon zaben na karshe dai jam’iyyun PDP da LP da wasu suka yi fatali da shi, bisa zargin magudi da saba dokar zabe, inda suka ce za su shigar da kara a gaban kotu.
Sai dai kuma daga cikin jam’iyyu 18 da ake da su a Najeriya, 11 sun nesanta kansu da boren da PDP ta jagoranta na ficewa daga cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a Abuja.