✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yau ake rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar, Bazoum

Karon farko da zababbun shugabannin kasar za su mika wa juna mulki

Sabon zababben Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum zai karbi ranstsuwar fara aiki a ranar Juma’a, 2 ga Afrilu, 2021.

Karon farko ke a Jamhuriyar Nijar da za a mika gwamnati tsakanin zababbun shugabannin kasar, inda Bazoum zai karbi ragamar mulki daga Shugaba mai barin gado, Mahamadou Issoufou.

Bazoum wanda shi ne tsohon Ministan Harkokin Wajen Jamhuriyar Nijar ya samu nasara ne a zagaye na biyun zaben Shugaban Kasar kasar da ya gudana a watan Fabrairu, 2021.

Abokin karawarsa kuma tsohon Shugaban Kasar, Mohammed Ousmanne ya kalubalanci sakamakon a kotu, amma ta tabbatar da nasarar Bazoum daga jam’iyyar PND Tarayya ta Shugaba Issoufou mai barin gado.

Tun daga samun ’yancin Jamhuriyar Nijar zuwa yanzu, Issoufou shi ne Shugaban Kasar na farko da ya kammala wa’adi biyu a jere yana mulkin ksar, daga 2011 zuwa 2021.

Bazoum wanda ake gani a matsayin dan lelensa ne, ya yi alkawarin ginawa a kan ayyukan da ya faro na yaki da ta’addanci da farfado da tattalin arzikin kasar wadda ke cikin mafiya talauci a duniya.

A watan Maris, Mahamadou Issoufou ya lashe kyautar Gidauniyar Mo Ibrahim a matsayin Shugaban Afrika wanda ya fi iya gudanar da mulki, duk da kasancewar Jamhuriyar Nijar matalauciya da kuma sauran matsalolin da suka yi mata dabaibayi.

Kasashen duniya da al’ummar Nijar wadanda Bazoum ke da farin a wurin wasunsu na jira su ga kamun ludayinsa da kuma yadda zai cika alkawuran da ya yi na yakin neman zabe.

Babban kalubalen Bazoum na farko shi ne daidaita al’amuran gudanar da kasar da ta fuskanci yunkurin juyin mulki daga sojoji, kwana biyu kafin ya hau kan karagar mulki.

Kasar tasa ta jima tana fama da matsalar tsaro da suka hada da ta’addancin mayakan Boko Haram da ISWAP da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai a kasar da makwabtanta na yankin Sahel.

Dubban fararen hula da sojoji sun kwanta dama sakamakon hare-haren ’yan bindiga a lokuta daban-daban a sassan Jamhuriyar Nijar.

A halin yanzu ’yan ta’adda sun gurgunta yanayin samar da wutar lantarki a wasu sassan kasar, suna kuma ci gaba da kai hare-hare a kan ma’aikata da nufin hana a gyara barnar da suka yi.

Uwa uba matsalar fatara da kasar ke fama da ita a yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar matsaloli tun bayan bullar annobar coronavirus da kuma faduwar farashin danyen mai wanda a yanzu yake kasar take samun kudade ta hanyarsa.

%d bloggers like this: