✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yaro mai shekara 4 ya mutu a rijiya a Kano

An ciro gawar yaron tare da mika ta ga mai unguwar Ilesha.

Wani yaro mai shekara hudu ya fada rijiya ya mutu unguwar Dawanau Ilesha Nawawu da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano a ranar Litinin.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

“Mun samu kiran neman agaji da misalin karfe 4:55 na yamma daga wani mai suna Aminu Sani Sha’aibu, inda muka tura jami’anmu da misalin karfe 5:20 na yamma,” a cwearsa.

Ya kara da cewa an cire gawar yaron daga rijiyar, kuma hukumar tana gudanar da bincike don gano dalilin mutuwarsa.

Abdullahi ya ce an mika gawar ga mai unguwar Ilesha Nawawu, Malam Musa Habibu.

Kazalika, ya bayar da lambobin kar-ta-kwanan hukumar don kai dauki idan wani abu ya faru, kama kamar haka 08107888878, 07051246833, 07026026400 da kuma 08098822631.