✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A wata uku yara miliyan 3 sun daina zuwa makaranta

Minista a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Emeka Nwajiuba, ya ce yara miliyan 10 ne ke gararamba ba sa zuwa makaranta a Najeriya. Ministan ya ce…

Minista a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Emeka Nwajiuba, ya ce yara miliyan 10 ne ke gararamba ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

Ministan ya ce hakan na nufin an samu karin yara miliyan uku da dubu 54 da ba su halartar makarantu a cikin shekara guda da ta wuce.

Hannun agogo ya kara komawa baya ke nan wajen yawan kananan yara marasa halartar makarantu a Najeriya a cikin rubu’in farkon 2021.

A watan Janairu, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ce yawan yara miliyan 10.1 marasa zuwa makaranta a 2019 ya ragu zuwa miliyan 6.946.

Amma, yayin kaddamar da shirinin inganta ilimi na Bankin Duniya (BEDSA) a Dutse, Jihar Jigawa, Nwajiuba ya ce: “Yara 10,193,918 marasa zuwa makarantu a Najeriya shi ne adadi mafi yawa a yankin Sahara.”

Nwajiuba dai bai bayyana abubuwan da suka haddasa karuwar yara marasa zuwa kamarantu ba.

Sai dai ya ce, muddin Najeriya na son magance matsalar, do wajibi ne sai ta inganta bangaren ilimi ta hanyar tunkarar matsalolin da ke hana yara halartar makaranta domin samun ilimi a matakin farko.

 

Dalilin rashin zuwan yara makarantu

Kakakin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Ben Goong, bai amsa kiran wakilanmu ba domin samun karin bayani game da abun da ya haddasa karuwar yawan yaran da ba sa zuwa makarantu.

Amma wani masani a fannin ilimi, Michael Ojunugwa, ya danganta matsalar da hare-hare da kuma sace dalibai da malami da ake yi a makarantu a Arewacin Najeriya.

“Idan ba a tashi tashe ba, za a kai lokacin da ilimi zai tsaya cik a Arewa saboda iyaye ba za su yarda ’ya’yansu su je su makaranta su kare da shan azaba a hannun ’yan bindiga da ’yan ta’adda ba,” inji shi.

Wani mai sharhi ka al’amuran al’umma, Suleiman Eshiotsekhai, ya ce: “Alkaluman UNICEF na shekara uku da suka gabata ya nuna yara miliyna 11 ne ba sa zuwa makarantu a Najeriya. Akwai bukatar ministan ya yi karin bayani.”

 

Jihohin da matsalar ta fi kamari

A cewar Minista Nwajiuba, Jihar Jigawa ita ce kan gaba wajen fama da matsalar, shi ya sa aka kaddamar da shirin a jihar, domin taimaka wa kokarin gwamnatin jihar na farfado da bangaren.

Ya ce baya ga Jagawa, wasu jihohi 16 da suka hada da Jihohin Arewa maso  Yamma da Arewa maso Gabas da kuma Neja, Ribas, Oyo da kuma Ebonyi, za su amfana da shirin.

Ministan ya nuna damuwa kan yawan yara marasa zuwa makaranta, inda ya ce johohin za su ci gajiyar shirin ne gwargwadon adadin yaran a jihohin.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihohi da na tararayya da masu rauwa da tsaki su hada hannu wajen magance matsalolin da ke tarnaki ga cigaban kasar.

Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce a yunkurin gwamnatinsa na magance matsalar, ta dauki malamai 1,393 aiki a 2018.