Wata tsohuwa ’yar shekar 72 da wasu mutum biyu sun rasu a sakamakon hatsarin motar fasinja da wata babbar mota a cikin dare a yankin Gbagada da ke Jihar Legas.
Hatsarin ya auku ne wata bas mai daukar mutum 18, cike da fasinja ta kwace a hanyarta ta zuwa Oshodi daga Ojo, inda ta yi karo da wata babbar mota.
- Yau za a yi jana’izar mahaifiyar Sanata Ahmad Lawan
- Yadda kananan yaran Arewa ke gararamba a Kudu da sunan neman kudi
Hukumar sufuri ta Jihar Legas LASEMA, ta ce, “Maza biyu da mace daya sun rasu nan take, wasu kimanin mutum bakwai kuma su samu raunuka.
“An garzaya da wadanda abin ya ritsa da su Babban Asibitin Gbagada”, inda aka kwantar da wasu daga cikinsu a sashen kula da lafiya ta gaggawa, in ji Babban Sakataren LASEMA Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu.
Ya sanar da haka ne a safiyar Lahadi, inda ya bayyana cewa bayan aukuwar hatsarin da dare ne suka samu kiran gaggawa, inda suka je wurin domin kai dauki.