✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kananan yaran Arewa ke gararamba a Kudu da sunan neman kudi

Ana kai su kudu a cikin motocin daukar dabbobi daga Arewa, wasunsu ba ba su ma san inda za su sauka ba

A baya ko manya da matasa suka ce za su je Kudu neman kudi, iyaye da dama ba su amincewa, saboda suna daukar haka a matsayin wani lasisi ne na lalacewa ga ’ya’yan nasu.

Don haka babu ma batun a ga samari masu matsakaitan shekaru sun nade kaya da sunan zuwa Kudu neman kudi balle a yi maganar kananan yara ’yan shekara 10 zuwa 15.

Sai dai a yanzu duk mutumin da ke zaune a Kudancin Najeriya na iya ganin yadda kananan yara maza da mata da suka fito daga Arewa suke gararamba a titunan Kudancin kasar nan.

Akasarinsu iyayen daki suke zuwa Arewa su kwaso su, su je da su domin yin barace-barace da sunan neman kudi.

Sai dai akwai yaran da sukan yiwo tattaki a karan-kansu, ba tare da sun san inda za su je ba, su dai kawai sun taho Legas, ko Kudu da sunan zuwa neman kuɗi ko aiki.

A irin haka ne Aminiya ta samu labarin wasu yara hudu masu karancin shekaru da suka taso daga Jihar Kano zuwa Legas a karshe aka iske su suna ta yin gararamba a babbar hanyar nan ta Legas daga Ibadan.

Sun tafi Legas ba su san inda za su ba

Wasu matasan Arewa da suke gudanar da harkoki a mashigar Legas daga Jihar Ogun a kusa da Karar Basi da ke kan iyakar jihohin Legas da Ogun ne suka kai wa yaran dauki bayan sun lura da halin da suke ciki.

Muhammad Fayama Jarimi, Shugaban ’Yan Kwamashon motocin bas a Tashar Isheri da ke daura da karar, ya shaida wa Aminiya cewa abin takaici ne yadda ake safarar yara kanana daga Arewa ba tare da mahukunta na sanya ido ba.

Ya ce ko a ranar Talatar makon jiya sai da suka kai wa wasu kananan yara dauki, wadanda wani direban babbar mota ya dauko su daga Kano ya zube su a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, inda yaran suka yi ta gararamba cikin yunwa da kuma rashin sanin inda za su dosa.

Ya ce, “Yaran masu ƙaracin shekaru, su huɗu da ba su wuce shekara 12 zuwa 15 ba, mun gan su ne suna gararamba bayan da wani direban babbar mota ya sauke su a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a shiyyar Wawa.

“Sun faɗa mana a wani masallaci suka kwana. Mun gan su cikin galabaita sai muka saya masu abinci.

“Sun faɗa mana daga Unguwar Fagge a Kano suke, kuma suna tallar ruwan leda ne a haka suka haɗa kudi Naira 5,500 suka bai wa direban babbar mota ya dauko su domin ya kai su Legas.

“Wannan abin takaici ne lura da yanayin da aka dauko su, da kuma yadda suka samu kansu.”

Ya ce ya kamata mahukunta su rika sanya ido a kan yadda ’yan kwamasho da direbobin manyan motoci ke gudanar da ayyukansu a tashar motoci na Kwanar Dawaki da ke Kano, domin su ne ke taimakawa wajen safarar kananan yaran daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya.

Yadda yaran ke zuwa Kudu

Aminiya ta zanta da yaran hudu masu suna Ibrahim Ali Fagge, Muhammed Kabir, Sani Musa da Hassan Abubakar, inda Sani Musa wanda shi ne babba a cikinsu ya ce sun yanke shawarar zuwa Legas ce domin su nemi kudi, saboda an fada musu an fi samun kudi a Legas.

Ya ce sun je tashar Kwanar Dawaki ce a Kano suka shiga babbar motar, bayan sun tara kudin motar ta hanyar tallar ruwan leda.

“A Unguwar Fagge muke, dama muna zuwa tallar fiya wata (ruwan leda) ne mu samo kudi mu kai gida sai a hada a saya mana abinci mu ci da kannenmu.

“Talla muke yi mu taimaki iyayenmu, cikinmu akwai wadanda suke da iyaye, akwai wadanda iyayensu sun rabu da juna.

“Talla duka muke yi, kuma da muka yanke shawara muka taho Legas ba mu sanar da iyayenmu ba.

“Sai dai mun sa abokanmu su fada musu bayan mun shiga mota mun taso, muka ce a sanar da iyayenmu mun tafi Legas” in ji shi.

Ya ce kwana hudu zuwa biyar suka yi a hanya a cikin babbar motar, kuma kafin a sauke su kudin hannunsu ya kare.

“Muna da yawa wadanda direban ya dauko, amma mu yara za mu kai 20, wasu cikinmu sun saba zuwa.

“Amma mu wannan ne zuwanmu na farko, da direban ya sauke mu cikin dare kowa sai ya kama gabansa ya tafi.

“To mu ba mu san inda za mu je ba, sai muka kwana a gefen hanya da gari ya waye muka kama tafiya sai wani mai babur ya gan mu ya dauke mu ya kai mu cikin kara, ya ce kudinmu Naira 800.

“Wani Bafullatani ne ya biya mana kudin sai muka je masallaci muka ci gaba da kwana a cikin karar, kafin daga bisani mu fito muna neman taimako.

“Yanzu so muke mu koma gida, domin mun zo Legas mun tarar da ita ba yadda muke jin ta ba, ba mu san kowa ba, ba mu da wajen kwana, abinci ma taimaka mana ake yi, don haka muke neman taimako don mu koma gida” in ji shi.

Malam Audu Dankamasho a sashin motocin bas homa a Isheri daura da karar Basi, ya shaida wa Aminiya cewa a kwanakin baya wani direba ya zube wasu kananan yara da ya dauko daga Kano.

“Direban ya dauko yaran su biyu ne ko kudin mota ba su da shi, sai ya zo nan da su ya ce tun daga Kano suke waya da wanda zai karbi yaran, amma da ya iso nan da su sai mutumin ya daina daga wayar kuma ya ki zuwa.

“Nan take na yi ta yi wa direban fada na ce yaya za a yi ya dauko yara masu kananan shekaru tun daga Arewa ya kawo su Kudu?

“Ana cikin haka sai muka nemi yaran muka rasa, wannan shi ne matsalar da ake fama da ita.

“A daidai lokacin da ake cikin mawuyacin hali na matsalar tattalin arziki da talauci a kasar nan, ana samun wasu ba-tagari na safarar yara kananan suna ci da guminsu” in ji shi.

Matsalar Arewa maso Yamma ce

Shi ko Muhammad Madu, shugaban na ’yan kamasho na manyan motoci a Karar Basi, ya shaida wa Aminiya cewa, direbobin manyan motoci da ke taso wa daga jihohin Katsina da Sakkwato da Zamfara da sauran jihohi Arewa maso Yamma ne suke yin safarar kananan yara daga Arewa suna kai su Kudu.

“Babban abin takaici shi ne yadda wadannan direbobin ke dauko mutane a cikin shanu ko awaki ko a saman kaya, musamman direbobin jihohin Katsina, Zamfara, da Sakkwato.

“Kuma a Tashar Kwanar Dawaki da ke Kano suka fi dauko su, amma ka ga direbobin da ke aiki a shiyyar Arewa maso Gabas ba sa daukar mutane a cikin manyan motocinsu.

“Muna kira ga direbobi su yi wa Allah su daina safara ko jigalar yara masu karancin shekaru, domin suna sanya yaran a cikin halin kaka[1]ni-ka-yi.

“Haka su ma mahukunta muna kira a gare su da su rika sanya ido,” in ji shi.

Muhammed Fayama ya jagoranci nema wa yaran taimakon kudi, inda ya ce sun sa su a mota domin a komar da su Kano, wato jihar da suka fito.

Akwai rashin kulawa

Binciken da Aminiya ta yi ta gano cewa daya daga cikin yaran dan asalin garin Gashuwa ne a Jihar Yobe, kuma wani dan sanda da ke aiki a garin Gashuwa da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa yaron yana bukatar kulawa ta musamman, lura da mawuyacin halin da ya samu kansa a ciki.

Ya ce, “Akwai zargin an samu yaron ne ba ta hanyar aure ba, kuma daga bisani mahaifiyarsa ta rasu.

“Suna zaune tare da ’yan uwansa uku. Shi ma mahaifin nasu Allah Ya yi masa cikawa, to ka ga mu a nan Arewa idan aka ce yaro ya samu ba ta hanyar ba aure ba, zai yi wuya ya samu kulawar kirki daga dangin iyaye, to halin da yaron ya samu kansa a ciki ke nan, kuma yanzu haka a karancin shekarunsa, rashin kulawar ya sa ya fara zama tantiri, domin yaron da bai wuce shekara 12 yanzu haka yana shan sholi, yana sace-sace.

“Ni kaina na yi aiki a kan laifuffukansa uku, to ka ga rashin samun kulawa ne ya jefa shi a wannan yanayi.

“Kuma idan ba a yi wa tufkar hanci ba, za a samu matsala” in ji shi.

Ya ce a kwakanin baya wani dan sanda ya sha alwashin daukar nauyin yaron inda ya sa shi a makaranta, kuma ya rika ba shi kudin makaranta, amma daga baya yaron ya ki zama.

“Akwai wani dan uwan baban yaron, shi ma yana kokari a kan yaron, amma ba ya da karfi.

“Don haka ire-iren wadannan yara suna bukatar kulawa domin ba su kariya daga zama bata-gari a nan gaba,” in ji shi.

Laifin iyaye ne –Sarkin Ogere

Sarkin Hausawan Ogere a Jihar Ogun, Alhaji Abdullahi Saminaka ya dora laifin ne a kan iyayen da suke barin ’ya’yansu kanana suna baro Arewa zuwa Kudu da sunan neman kudi ko neman aiki.

“Ya ce akwai iyayen da wasu ke zuwa su yi masu romon-baka su yaudare su su karbo ’ya’yansu suna yin bara da su.

“Ya bayyana  cewa ana zuwa ana neman kudi da yaran ana tura wa iyayen wani abu daga cikin abin da ake samu. Wasu kuma yaran suna tahowa ne ba da sanin iyaye ba.

“Amma duk yaron da zai taso daga Arewa ya taho Kudu, kai ka san ba ya samun kulawar iyaye,” in ji shi.

Shawara ga iyaye da mahukunta

Sarkin Hausawan ya kara da cewa, iyaye su daina bari ana yi masu romon-baka, domin yaran suna samun kansu a mawuyacin hali, ta yadda ko wajen da za su kwanta mai kyau yakan gagare su.

Kuma ya yi kira ga mahukunta su sanya ido a kan yaran Arewa da ke zuwa Kudu suna gararamba, inda ya ja hankalin mahukuntan Arewa su daina kawar da idanu game da yadda ake safarar kananan yara daga Arewaci zuwa Kudancin kasar nan.