✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a yi jana’izar mahaifiyar Sanata Ahmad Lawan

Mahaifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ta rasu tana da shekaru 86

A ranar Lahadin din nan za a yi jana’izar mahifiyar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, wato Hajiya Halima (Baba) Ibrahim.

Allah Ya yi wa Hajiya rasuwa ne ranar Asabar tana da shekaru 86 a duniya a gidanta da ke garin Gashua a Karamar Hukumar Bade ta Jihar Yobe.

Kakakin tsohon shugaban majalisar, Ezrel Tabiowo, ya sanar da cewa, “za a gudanar da Sallar Jana’aizar ce a Babban Masallacin Garin Gashua da ke Fadar Sarki Gashua.”

Sanata Ahmad Lawan shi ne shugaban Majalisar Dattawa na karshe kafin mai ci a yanzu, Sanata Godswill Akpabio.

Ya shekara 24 a matsayin dan majalisar dokokin Najeriya tun daga shekarar 1999 inda sau shida yana lashe zabe.

Daga 1999 zuwa 2003 ya kasance dan Majalisar Wakilai, kafin likafarsa ta daga zaben 2003, inda ya lashe zaben Sanatan Yobe ta Arewa, kujerar da yanzu karo na bakwai ke nan yana lashewa.