Kotu ta tabbatar da Bashir Macina a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC a kujerar Sanatan Yobe ta Arewa — mazabar Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan — a zaben 2023.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Damaturu, hedikwatar Jihar Yobe, ta tabbatar da halascin zaben dan takarar sanatan da jam’iyyar APC ta gudanar, wanda Bashir Macina ya lashe.
- Dokar haramta daukar makami na nan daram —Garba Shehu
- Masu sharar titi sun samu karramawa da kyaututtuka daga Gwamnatin Kano
Ta kuma soke zaben dan takarar sanatan mazabar da jam’iyar ta gudanar daga baya, wanda Ahmed Lawan ya lashe, da cewa haramtacce ne.
A ranar 28 ga watan Mayu ne APC ta gudanar da zaben dan takarar sanatan, wanda Macina ya lashe, a lokacin Ahmad Lawan yana neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Bayan ya sha kaye ne ya nemi komawa kan kujerarsa ta dan Majalisar Dattawa, lamarin da ya haifar da takaddama a jam’iyyar ta APC, musamman ma bangaren Macina.
Bayan yunkusin shawo kan Bashir Macina ya janye masa ne Macinan ya bayyana cewa ba zai taba janye wa wani ba, hasali ma, babban burinsa a rayuwa shi ne zama sanatan mazabar.
Bayan an jima ana kai ruwa rana, jam’iyyar ta gudanar da wani zaben dan takarar kujerar, wanda Ahmad Lawan ya lashe — lamarin da a kai su gaban kotu
Amma yanzu kotu at ayyana Bashir a matsayin halastaccen dan takarar sanatan Yobe at Arewa.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar da sunayen ’yan takarar Majalisar Tarayya da sauran kujeru na zaben 2023.
Sai dai ba ta fitar da sunan dan takarar APC a kujerar sanatan Yobe ta Arewa ba saboda wannan dambarwa.