Iyalan wata dattijuwa da suka nema suka rasa sun shiga fargaba bayan gano gawarta a cikin wani maciji.
Lamarin na zuwa ne bayan kumburin ciki ya bayyana sosai a kasurgumin maciji — kafin dangin tsohuwar su gano cewa maciji ya haɗiye kakarsu a cikinsa.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa
- Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja
Iyalan matar da ta ɓace sun bi sawun macijin zuwa wani mai yawan ciyayi a kudancin Sulawesi na kasar Indonesia.
’Yan yankin sun tsorata matuka lokacin da suka ga maciji mai tsawon kafa 26 ya yi nauyi da wani babban kumburi a cikinsa.
A lokacin da suka farka cikin macijin, sun gano gawar matar mai suna Hasia mai shekara 66, wadda ta bata a lokacin da take komawa gida daga wurin aikinta a wata gonar roba.
Ana kyautata zaton macijin ya fito ne daga dogayen ciyayin ya sari kafarta, wanda hakan ya sa ta faɗi.
Ɗan matar mai suna Nurdin, ya ce danginsa da ke cikin damuwa, sun kaddamar da bincike lokacin da dare ya yi, bayan da suka lura tsohuwar ba ta dawo gida ba.
Sun yi cigiya kafin su far wa macijin da misalin ƙarfe 9 na dare.
Sai suka sari macijin, suka buɗe cikinsa, inda suka tarar da gawar Hasia a cikinsa.
Nurdin ya razana, inda ya ce: ‘Wannan abu ne mai ban tsoro.
“Na san mutuwa ce mai raɗaɗi ga mahaifiyata, kodayake macijin ya mutu.
“Ba zai taɓa dawo da ita ba. Yanzu muna addu’ar Allah Ya jikan ta da rahama.
Ipda Zakaria, Shugaban ‘yan sandan PituRiase, ya ce: ‘Yanzu haka, ana shirin yi wa matar jana’iza.’
“Saboda haka, muna kira ga mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan wajen tafiya, domin an san cewa akwai manyan macizai a dajin.”