Wasu mutane da ba a tantance su wane ne ba, sun yi wa wata yarinya mai suna Amina Idris ’yar shekara shida fyade har sai da ta mutu a Kaduna.
Wakiliyar Aminiya a Kaduna ta ruwaito cewa an bayar da labarin batar yarinyar da misalin karfe 4.30 na yammacin Lahadi a yankin Mararaban Jos da ke cikin jihar.
- El-Rufai ya kori duk ma’aikatan jinya ’yan kasa da mataki na 14
- ’Yan daba sun far wa masu zanga-zangar Kaduna
- Matakan nada Khalifan Tijjaniyya — Sheikh Dahiru
Sai dai daga biasni an gano ta da misalin karfe 8 na yammacin Lahadin cikin daji, da raunuka a baki da hancinta.
Ganau sun ce sun ga wadansu mutum biyu sanye da bakaken kaya suna haska tocila a daidai wajen da aka gano yarinyar.
Amma wacce ta kafa Gidauniyar Arridah, Hajiya Rabi Salisu da ta tabbatar da lamarin ta ce an binne yarinyar ne a ranar Litinin da karfe 6 na yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Hajiya Rabi wacce ta dauki gabaran tabbatar da adalci a lamarin ta ce, “Likita ya tabbatar da cewa an yi wa yarinyar fyade ta duburarta kuma daga karshe ta yi da zubar da jini har ta mutu.
“Bayan bincike, sai aka gano cewa yarinyar an yi lalata da ita da karfi ta dubura wanda ya kai ga mutuwarta.
“Duk da cewa iyayen yarinyar sun ce sun yafe abin da aka yi wa ’yarsu saboda tsoron bata musu suna, gidauniyata ta dauki lamarin kuma ana ci gaba da bincike. Mun kai rahoton lamarin ga ’yan sanda kuma sun fara bincike.”
A watan Satumban bara, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta zartar da kudurin dokar dandaka tare da kashe ga duk wanda ya yi wa yaro fyade da ke kasa da shekara 14.