✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar shekara 13 ta zargi mahaifi da yi mata fyade

Wata yarinya mai shekaru 13 kacal a duniya, ta zargi mahaifinta, Kazeem Olapade da yi mata fyade a yankin Ido-Osun na Karamar Hukumar Egbedore a…

Wata yarinya mai shekaru 13 kacal a duniya, ta zargi mahaifinta, Kazeem Olapade da yi mata fyade a yankin Ido-Osun na Karamar Hukumar Egbedore a Jihar Osun.

Jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan Jihar, Yemisi Opalola ne ya sanar da hakan yayin zantawa da Aminiya ranar Asabar a birnin Osogbo.

Mista Yemisi ya bayar tabbacin cewa za a gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin.

Yarinyar ta bayyana cewa mutuwar auren da ke tsakanin iyayenta ya sanya take zama gida daya tare da mahaifinta.

Ta ce mahaifin nata ya yi mata barazana a kan kada ta labartawa kowa abin da ya faru amma daga bisani ta yanke shawarar fada wa mahaifiyarta halin da take ciki.

A cewarta, “Mahaifina ya rufe min baki da matashin kai yayin da yake yi min fyade kuma bayan ya gama na tsinci kaina cikin jini sannan ya yi min barazana a kan kada na kuskura na fada wa kowa.”

Yarinyar ta ce mahaifin nata wanzami ne amma daga baya ya koma makidin ganga kuma a yanzu haka yana da gidaje hudu a Osogbo, babban birnin Jihar.

Sai dai yarinyar wacce ’yar aji daya ce a makarantar sakandire bata fayyace lokacin da wannan lamari ya faru ba.

Aminiya ta ruwaito cewa a karon farko an shigar da korafin wannan lamari ga hukumar tsaron cikin gida ta hanyar wata kungiya mai zaman kanta, inda daga bisani aka mika lamarin a hannun hukumar ’yan sanda.