✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yar Sarki Fahd na Saudiyya ta rasu

Bayan Sallar La'asar za a yi jana'izarta Masallacin Imam Turki Bin Abdullah da ke Riyadh

’Yar margayi Sarki Fahd na kasar Saudiyya, Gimbiya Lolwah Bint Fahd Bin Abdulaziz Al Saud, ta riga mu gidan gaskiya.

A ranar Tatala, 19 ga watan Afrilu, 2022 za a gudanar da Sallar Jana’izar Gimbiya Lolwah, bayan Allah Ya yi mata rasuwa a ranar Litinin, wadda ta kasance 17 ga watan Ramadan din da muke ciki.

Masarautar Saudiyya ta sanar cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayiyar a Masallacin Imam Turki Bin Abdullah da ke Riyadh, babban birnin kasar, bayan Sallar La’asar.

Tuni Sarakunan kasashen Larabawa da sauran sassan duniya suka shiga mika ta’ziyyarsu ga Sarki Salman na Saudiyya game da rashin Gimbiya Lolwah.

Sarkin Oman, Sultan Haitham Bin Tarik, ya mika sakon ta’aziyya ga Sarki Salman da iyalan gidan Sarautar Saudiyya, yana addu’ar samun rahama ga marigiyar da kuma juriya ga iyalan gidan.