Mace ta farko kuma ’yar Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala na gab da zama Darakta-Janar na Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO).
Okonjo-Iweala, tsohuwar Ministar Kudi da Tattalin Arziki ta Najeriya ta samu goyn bayan 104 daga cikin mambobin WTO 164.
- Dangote ya goyi bayan Okonjo-Iweala a WTO
- Okonjo-Iweala ta kai matakin karshe a neman shugabancin WTO
“A cikin ‘yan takaran, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala daga Najeriya ce ke da gagarumar damar samun amincewar kowa. Nan gaba za a fara tattaunawa kan abin da za a yi na gaba”, inji Shugaban Babban Zauren WTO, David Walker, kamar yadda Kakakinsa Keith Walker ta ruwaito shi bayan zamansu da suka yi a ranar Talata.
Da haka, za ta kafa tarihin zama mace ta farko a duniya kuma mutum na farko daga nahiyar Afirka da ya zama Shugaban WTO.
Ta samu rinjayen ne bayan ganawar sirrin da kungiyar ‘Troika’ karkashin jagorancin Walker jakadan kasar New Zealand, mai fada a ji a WTO ta yi da mambobin cibiyar.
Hakan ya ba ta damar samun rinjaye a kan abokiyar hamayyarta tilo, Ministar Zuba Jari ta kasar Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee.
Ranar Laraba, 28 ga Oktobo 2020 Troika ke sanar da zamanta Darakta-Janar ta WTO da amincewar mambobin cibiyar 164.
- WTO: Okonjo-Iweala ta kafa tarahi
Ta dare kujerar ne a daidai lokacin da cibiyar ke cika shekara 25 kuma ita ce mace ta farko a fadin duniya da za ta jagoranci cibiyar.
Shugabancin da ta samu ya sa ta zama mace ta farko a duniya kuma mutum na farko daga nahiyar da ya zama Shugaban Cibiyar Kasuwanci ta Duniya.
Ta hau kujerar ne kafin cikar wa’adin ranar 7 ga watan Nuwamba na maye gurbin Roberto Azevedo dan kasar Brazil, wanda ya yi sauka daga mukaminsa a WOT a watan Agusta, shekara guda kafin cikar wa’adinsa.
- Goyon bayan da ta samu
Manyan kasashen duniya sun ki bayyana wanda suke boyon baya a cikin ‘yan takarar a fili duk da cewa wasu kasashen Afirka da yankin Caribbean sun bayyana goyon bayansu ga Okonjo-Iweala.
A gida Najeriya ma, Shugaba Buhari da babban attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote sun bayyana goyon bayansu ga da tsohuwar ministar kudin.
A wani sako da ta wallafa a baya-bayan nan, ta ce, “Ina matukar godiya da samun goyon baya domin zama Daraktar-Janar na WTO daga manyan shugabanni a duniya irinsu Mary Robinson, Mo Ibrahim, Aliko Dangote, Strive Masiyiwa, (da sauransu).”
A ranar Talata Tarayyar Turai ta sanar da goyon bayanta ga ‘yar Najeriyar.
Kazalika kungiyar Tarayyar Afirka dungurungun da kasashe da dama daga yankin Pacific da Asiya sun goyin bayan ta jagoranci
Kwarewar Ngozi Okonjo-Iweala
Ngozi Okonjo-Iweala mai shekara 66, ita ce mace ta farko da ta zama Ministar Kudi a Najeriya kafin daga baya ta jagoranci ma’aikatar Harkokin Waje.
Tsohuwar ministar ta shafe shekara 25 tana aiki a Bankin Duniya a matsayin kwararriya a tattalin arziki da gudanar da kudade na kasa har ta zama Manajan-Darekta, a Bankin Duniya.
A halin yanzu tana daga cikin Majalisar Daraktocin Twittter kuma babbar jakadiya ce a Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) kan yaki da COVID-19.
Aikin da ke gabanta a WTO
Babban aikin da ke gabanta a WTO shi ne yin gyaran fuska ga manyan kararrakin da cibiyar ta daukaka.
Cibiyar ta samu tasgaro a yunkurin nata bayan Shugaban Amurka ya tadiye ta saboda rashin alkalai.
Wani babban aikin da ke gabanta kuma shi ne shiryawa da kuma gudanar da babban taron kasuwanci a 2021.