✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yar kwallon Kamaru ta mutu a lokacin atisaye

Hukumar shirya kwallon kafa a Kamaru (FECAFOOT) ta bayar da sanarwar rasuwar golan kungiyar kwallon kafa ta mata Jeanie Christelle Djomnang a lokacin da take…

Hukumar shirya kwallon kafa a Kamaru (FECAFOOT) ta bayar da sanarwar rasuwar golan kungiyar kwallon kafa ta mata Jeanie Christelle Djomnang a lokacin da take atisaye a kulob dinta mai suna Femina Stars na Ebolowa da ke Kamaru.
’Yar kwallon ta rasu ne kwanaki biyu kacal da rasuwar wani dan kwallon Kamaru da ke buga kwallo a Romaniya Patrick Eken a ranar Lahadin da ta wuce.
Rahoton ya nuna dukkan ’yan kwallon biyu sun rasu ne sakamakon bugun zuciya (heart attack).
An ce Djomnang ta yanke jiki ta fadi ne a lokacin da suke atisaye a kokarin da suke yi na fafatawa da wani kulob mai suna Club de Lounres Minproff.
Rahoton ya ce ’yar kwallon ta rasu ne jim kadan bayan ta yanke jiki ta fadi ba tare da an taba ta ba inda aka garzaya da ita asibiti amma kafin likitoci su ceci rayuwarta rai ya yi halinsa.
Shi kuwa dan kwallon Kamaru Patrick Eken ya rasu ne a ranar 7 ga wannan wata da muke ciki a Romaniya a lokacin da yake yi wa kulob dinsa Dinamo kwallo a daidai minti na 70. An ce kulob dinsa yana fafatawa ne da na bitorul a gasar rukunin Romaniya a lokacin da al’amarin ya faru.
Idan za a tuna kimanin shekara 13 kenan, watau a ranar 26 ga watan Yunin 2003 irin haka ta faru da shahararren dan kwallon Kamaru Marc bibien Foe inda shi ma ya yanke jiki ya fadi a lokacin wata gasar kwallo a Faransa.