‘Yar Gwamnan Kano, Asiya Abdullahi Umar Ganduje, ta maka tsohon mijinta, Alhaji Inuwa Uba a gaban kotun majistare da ke Sabon Gari a jihar, bisa zarginsa da lakada mata duka da kuma cin zarafinta.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Abdu Aboki ya bayar da belin wanda ake zargi bisa wasu sharuda tare da dage shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Mayu, 2023.
- Buhari ya nada Oluwatoyin Madein a matsayin sabuwar Akanta-Janar ta Kasa
- An kama tirela makare da naman jaki na N23m a Kebbi
Mai gabatar da kara wanda jami’in kotun, Nura Ahmad Yakasai, ya wakilta, ya shaida wa kotun cewa a lokacin da tsofaffin ma’auratan suke zaune tsohon mijin Asiya Ganduje ya ci zarafinta tare da lakada mata duka.
Sai dai wanda ake kara ya musanta zargin da ake masa na na tilastawa da tayar da hankali da cin zarafi da yin kutse.
Lauyansa, Barista Hashim Mai-ulu ya nemi kotun da ta bayar da belin sa dogaro da sashen na 36 na kundin laifukan final kod.
Alkalin kotun ya bayar da belin wanda ake zargin bisa wasu sharuda tare da dage sauraren shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Mayu 2023.
A baya Asiya Ganduje ta maka tsohon mijin nata a gaban kotun shariar Musulunci, inda ta nemi kotun ta datse igiyar aurensu bisa dalilin cewa ta gaji da aurensa.
Kotun ta kashe auren a tsarin Khul’i bayan da matar ta fanshi kanta ta hanyar mayar masa da sadakinsa na Naira dubu 50.