Wata matashiya ’yar ƙasar China da ta gamu da ranar da ta fi kowace rana farin ciki a rayuwarta ta koma mafarki mai ban tsoro bayan mijinta ya nemi a yi masa gwajin mahaifa saboda sanin fatar jaririn da suka haifa mai duhu (baƙar fata).
A baya-bayan nan Jaridar China Times ta ƙasar China ta ba da labarin wani lamari mai ban mamaki na wata mata ’yar ƙasar a yankin Shanghai mai shekara 30 da ke da burin ci gaba da aurenta bayan ta haifi jariri baƙar fata ta hanyar tiyata.
- A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga
- An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo
Matar ta shiga kafafen sada zumunta na zamani, inda ta ba da labarinta mai ban tausayi sannan ta nemi sauran iyaye mata su ba ta shawarar yadda za a shawo kan lamarin.
Ta yi iƙirarin cewa, bayan ta haihu, lokacin da mijinta zai haɗu da ɗansa a karon farko, sai kawai ya kalle shi cikin ruɗewa, ya ƙi yarda ya ɗauke shi.
Matar ta yarda cewa ita ma ta yi mamakin haihuwar baƙar fata kuma ta ji kunya lokacin da ta riƙe jaririn, tana ta cewa, “ba ta taɓa zuwa Afirka ba kuma ba ta san wani baƙar fata ba”.
Ba wai kawai rashin nuna farin ciki ne mijin matar bai nuna ba, ya kuma ya nemi a gwada halittar ɗan don tabbatar da cewa ɗansa ne.
Rubuta labarin a kafar sada zumunta ta Weibo da matar ya yi ta karaɗe intanet cikin sauri, kuma da yawa sun tabbatar mata cewa akwai kamanni sai dai launin fata mai duhu ta jaririn.
“Wannan al’amari na iya faruwa a zahiri saboda fatar jikinsu tana iya zama ba ta da kyau ko kuma jininsu ba shi da kyau.
Lamarin irin hakan na iya faruwa, inda akan samu fata mai duhu daga uwa farar fata,” in ji wani ƙwararre da ya yi martani.
“Wannan na iya faruwa kowane lokaci. Launi fata zai iya yin haske zuwa wani lokaci,” in ji wani.
Wasu kuma sun fi damuwa da halin miji da nuna rashin amincewa da mahaifiyar jaririn, wanda ɗan farko ne, inda suka shawarce ta da ta yi doguwar tattaunawa da mijin game da dangantakarsu bayan an yi gwajin halittar jaririn.