✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yar aiki ta rataye kanta a Kano

Har yanzu jami'an tsaro ba su gano dalilin da yasa 'yar aikin ta rataye kanta ba.

Wata ’yar aikin gida mai shekara 16 daga Jihar Gombe ta rataye kanta a gidan da take aiki a Kano.

An tsinci gawar budurwar ce a rataye a cikin dakinta da misalin karfe 10 na dare a gidan mutanen da ke matsayin iyayenta na riko.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cawa ba a gano musabbabin rasuwarta ba, amma ganin gawarta a ranar Asabar ya ta da hankalin mazauna a yankin Gidan Zoo, inda lamarin ya faru.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce jami’an tsaro su dauke gawar budurwar zuwa Babban Asibitin Murtala.

Ya ce ’yan sanda sun fara bincike kan lamari domin gano abin da ya jawo rasuwar ’yar aikin.